Kasar Amurka ta Harbo Wani Jirgi da ke Shawagi a Sararin Samaniyarta
Kasar Amurka ta Harbo Wani Jirgi da ke Shawagi a Sararin Samaniyarta.
Amurka ta ce tana ƙoƙarin tattara tarkacen wani abu mai kama da jirgi jirgi da ba a san asalinsa ba bayan da ta harbo shi kan tekun Arctic.
Abin wanda aka ce ya kai girman ƙaramar mota, yana shawagi ne a sama kuma ana ganinsa a matsayin barazana.
A yanzu dai babu wani abu da ya nuna cewa abin da aka harbo din yana aikin sa ido ne.
Wani kakakin Pentagon bai yi wa yan jarida ƙarin bayani ba, game da inda jirgin ya fito ko ma maƙasudin kasancewarsa a sararin samaniyar Amurka.
Ministar tsaron Canada Anita Anand ta ce za su taimaka wajen tura jiragen da za su bi diddigi.
An dai fara ganin abun ranar Alhamis da daddare, to sai dai jami’ai ba su bayyana lokaci ba.
Hakan na zuwa ne mako guda bayan da Amurkan ta harbo wani balan-balan ɗin ƙasar China da aka zarga da leƙen asiri, da aka gani yana shawagi a sararin samaniyar Amurkan.