Labarai

Bankuna sun karkatar da sabbin takardun kudi Naira biliyan 4.3 a Yobe

Bankuna sun karkatar da sabbin takardun kudi na Naira biliyan 4.3 a Yobe – Babban jami’in kula da harkokin kananan kudi ya yi zargin.

Manajan Darakta na Bankin Micro Finance na Yobe Sheriff Muhammad Almuhajir ya yi zargin cewa an karkatar da kudaden da babban bankin Najeriya CBN ya raba wa bankunan jihar da suka kai Naira biliyan 4.3.

MD ya yi wannan zargin ne a cikin wani hoton bidiyo na dakika 4:31 da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata. “Ina so in fada muku cewa, na samu tabbataccen labari cewa babban bankin Najeriya reshen Damaturu ya raba wa bankunan jihar Yobe zunzurutun kudi har naira biliyan 4.3.

“Kuma sama da Naira miliyan 700 na kudin an yi wa jami’an P.O.S ne,” inji shi. Almuhajir ya kuma yi zargin cewa Naira biliyan 4.3 da aka rabawa bankunan kasuwanci ba sa yaduwa a jihar, don haka ya zargi wasu manajojin bankin da karkatar da kudaden daga jihar.

“Amma tambayar da nake son yi anan ita ce, ina wannan kuɗaɗen?”, ya tambaya. Ya yi zargin cewa sabbin takardun Naira da ake yawowa a fadin jihar ba su kai Naira biliyan daya ba. MD na bankin ya bayar da hujjar cewa ko da ATMs za su rika ba da tsabar kudi a kowane minti daya, ba za a iya fitar da adadin a cikin mako guda ba. “Nawa ne yawan al’ummar jihar Yobe?

“Bankunan kasuwanci nawa muke da su a jihar nan? ATM nawa muke da shi?” Ya tambaya.

Ya kara da cewa, jihar Yobe ba ta da injinan Automated Teller Machines, (ATMs) har guda 50, domin mutane su ciri N4.3. biliyan a cikin kankanin lokaci.

Almuhajir ya kuma bayar da hujjar cewa wasu ma’aikatan Points of Sale suna samar da ayyuka masu kyau fiye da yawancin bankunan kasuwanci da ke aiki a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu