Labarai
Yau 10 Febreru Darajar Naira Ta Ɗaga Kan Dala A Kasuwar Musayar Kudi

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai Naira ta samu armashi a kasuwar musayar kudi, inda aka sauya kowace dala akan Naira 461.10 a kasuwar musayar kudi.
Alkaluman ya nuna samun karuwa da kashi 0.02 bisa dari idan aka kwatanta da na 461.17 da aka yi musanya a ranar Laraba.
Farashin a kasuwar musayar kudin ya tashi akan Naira 461.25 a kowace dala a ranar Alhamis.
Canjin naira 462 zuwa Dala shine mafi girman farashin da aka samu a cinikin yau kafin ya daidaita akan N461.10.
Ana canzar da Naira kan dala 439.96 zuwa dala a kasuwar a ranar Alhamis, an sayar da jimillar dala miliyan 40.24 a bangaren masu saka hannun jari da masu fitar da kayayyaki a hukumance.