Siyasa

Idan Kun Zaɓe Ni Zaman Lafiya Zai Dawo -Atiku Abubakar Yayi Alkawari

Idan Kun Zaɓe Ni Zaman Lafiya Zai Dawo -Atiku Abubakar Yayi Alkawari.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya tabbatarwa da mutanen jihar Yobe zai dawo da zaman lafiya a jihar idan aka zaɓe shi.

Atiku ya kuma yi alƙwarin buɗe iyakokin dake tsakanin Nijar da Yobe domin samar da hanyar wucewar mutane da kayan amfanin gona. Rahoton jaridar MANUNIYA Ta tabbatar

Da yake magan a wajen yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a jihar Yobe, Atiku yace idan aka zaɓe shi zai samar kuɗi domin mata da matasa su kama sana’o’i.

A kalamansa:

Idan kuka zaɓi PDP, zaman lafiya zai dawo a Yobe. Zamu tabbatar da cewa mun buɗe makarantun mu, ta yadda ƴaƴan mu za su cigaba da zuwa makaranta.

Mun kuma yi alƙawarin zamu samar da jari ga matasa da mata ta yadda zasu fara kasuwancin su, domin samun damar yin rayuwa mai inganci.

Mun yi alƙawarin sake buɗe iyakokin ƙasar nan ta yadda kasuwancin dake tsakanin mu da makwabtan mu zai bunƙasa yadda ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button