Siyasa

Abin da Buhari ya fadawa ‘yan Najeriya game da Tinubu a Sokoto

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis ya yi kira ga al’ummar Sokoto da su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2023.

Buhari, wanda ya yi magana a taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a Sokoto, ya ce Tinubu ne mai rike da tutar jam’iyyar, inda ya kara da cewa, “duk muna goyon bayansa.

A yau, muna Jihar Sakkwato, Kujerar Halifanci, domin yi wa dan takarar jam’iyyarmu, Tinubu kamfen.

“Shi dan takarara ne, ya kamata mu zabe shi, mu sanar da wadanda ba sa nan tare da mu. zabin APC shine Tinubu kuma muna addu’ar shi ne zai jagoranci kasarmu,” inji shi.

Shugaban ya kuma yabawa al’ummar jihar bisa yadda suka nuna kauna da karimci tun zuwansa jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button