Real Madrid za ta Buga Wasan Karshe da Al Hilal a Club World Cup
Real Madrid za ta Buga Wasan Karshe da Al Hilal a Club World Cup.
Real Madrid za ta buga wasan karshe a Club World Cup, bayan da ta doke Al Ahly 4-1 ranar Laraba a Morocco.
Mai rike da kofin zakarun Turai ta ci kwallayen ta hannun Vinicius Junior da Federico Valverde da Rodrygo da kuma Sergio Arribas Calvo.
Ita kuwa Al Ahly mai kofin zakarun Afirka ta ci kwallonta ta hannun Ali Maaloul a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Real wadda ke fatan daukar kofi na takwas jimilla za ta fuskanci Al Hilal ta Saudi Arabia ranar Asabar a Prince Moulay Abdellah a birnin Rabat, Morocco.
Al Hilal ita ce mai rike da kofin zakarun Asia, wadda ta ci Flamengo ta Brazil a karawar daf da karshe ranar Talata.
Kungiyar Saudi Arabia ta yi nasara a kan ta Brazil da cin 3-2.
Al Hilal ta fara da yin nasara a kan Wydad Casablanca a bugun fenariri a zagaye na biyu a gasar kofin duniya ta zakarun nahiyoyi.
Jadawalin wasannin Club World Cup:
Zagayen farko:
Al Ahly da Auckland City (3-0).
Zagaye na biyu:
Seattle Sounders da Al Ahly (0-1)
Wydad Casablanca da Al Hilal (1-1; 3-5 a bugun fenariti)
Karawar daf da karshe:
Flamengo da Al Hilal (2-3)
Al Ahly da Real Madrid (1-4)
Wasan neman mataki na uku: 11 ga watan Fabrairu
Al Ahly da Flamengo
Wasan karshe: 11 ga watan Fabrairu
Real Madrid da Al Hilal