An Rufe Wasu Bankuna Gaba Daya a Akure Babban Birnin Jihar Ondo
An Rufe Wasu Bankuna Gaba Daya a Akure Babban Birnin Jihar Ondo.
Bankunan kasuwanci sun dakatar da ayyukansu gaba daya a Akure babban birnin jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Jaridar MANUNIYA ta ruwaito cewa dukkanin bankunan da wakilanta suka ziyarta a titin Oba Adesida da kuma Alagbaka a babban birnin jihar, kofofinsu na kulle.
Sai dai ta ce akwai tarin jama’a masu mu’amulla da bankin da suke tsaye curko-curko a wajen bankunan suna zaman jiran tsammani.
Daya daga cikin mutanen mai suna Jimoh ya bayyana cewa tun karfe 7:30 nsf (na safe) yake wurin.
Mutumin ya ce jami’an tsaron bankunan sun gaya masa cewa an rufe bankunan ne saboda tsoron kai musu hari.
kamar dai sauran sassan jihar ta Ondo can ma a garin Ikare-Akoko da ke yankin karamar hukumar Akoko Northeast ba a bude bankunan ba ga jama’a.
Jama’a na fama da wahalhalu sakamakon matakin Babban Bankin kasar na sauya fasalin wasu daga cikin manyan takardun kudin kasar na 1,000 da 500 da kuma 200.
Bankin ya sanya wa’adin daina karbar takardun a tsakanin jama’a zuwa ranar 10 ga watan nan na Fabrairu, to amma kuma a jiya laraba Kotun Kolin kasar ta yanke hukuncin shari’ar da gwamnonin jihohin Kogi da Kaduna da kuma Zamfara suka shigar gabanta kan hana wa’adin.
Kotun ta yanke hukuncin dakatar da aiwatar da shirin Bankin na hana mu’amulla da kudin har sai ta yanke hukunci na karshe a shari’ar wadda ta dage zuwa ranar 15 ga watan na Fabrairu.