Kungiyar Malamai Ta kasa NUT tace ba zata Yadda Da cire Tallafin mai ba Duba da irin Wahalar da zai Jefa Talakawa
Kungiyar Malamai Ta kasa NUT tace ba zata Yadda Da cire Tallafin mai ba Duba da irin Wahalar da zai Jefa Talakawa.
Kungiyar malamai ta kasa a Najeriya (NUT) ta ce bata goyon bayan yunkurin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ke shirin yi.
Shugaban kungiyar na kasa Titus Amba, shi ne ya bayyana haka jiya Litinin a Abuja a wajen taron kungiyar na shekarar 2023, rahoton MANUNIYA.
Ya yi kira da a kara bibiyar tsarin tallafin ”da nufin kawar da cin hanci daga cikin tsarin.” Gwamnatin tarayya ta ce za ta daina biyan kudin tallafin man fetur daga karshen watan Yuni bayan biyan naira tiriliyan 3.36 na tallafin tsahon wata shidan farko na shekarar nan.
Cire tallafin man fetur zai kawo wahala da kuncin rayuwa, Amba
Amma shugaban na NUT a jiya ya bayyana cewa tsadar man fetur da sauran abubuwan da suka shafi danyen mai ya janyo tsadar kayayyakin wanda ya jawo kunci ga dukkan masu neman kudi a kasar nan.
Amba ya kuma bayyana cewa kungiyar za ta dau mataki kan duk jihar da bata zartar da dokar mafi karancin albashi N30,000 ga malaman makaranta ba.
Ya ce:
”Mun tattauna sosai da gwamnatocin jihohi kan batun mafi karancin albashi N30,000 , mun kuma shigar da korafe-korafe ga kungiyoyi game da wasu jihohi da basu bada hadin kai ba.”
Ya ce gwamnatin Jihar Kaduna ta yi karin albashi ne ga iya malaman sakandire ba tare da yi wa malaman firamare karin ba.
Ya ce matsalolin tsaro, da suka janyo hare-hare a makarantu da garuruwa, sun yi sanadiyar mutuwar malamai da dalibai tare da lalata makarantu.