Emefiele Ya Amin Ce Zai Ba INEC Cikakken Haɗin kai Da Goyan Baya Dari Bisa Dari
Emefiele Ya Amin Ce Zai Ba INEC Cikakken Haɗin kai Da Goyan Baya Dari Bisa Dari.
Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya tabbatar wa hukumar zaɓen Najeriya INEC cewa babban bankin ba zai yi wani abu da zai kawo cikas ga zaɓen 2023.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito Mista Emefiele yana bayyana hakan bayan ya karɓi baƙuncin shugaban na INEC Mahmood Yakubu.
Shugaban na INEC tun da farko ya shaida wa shugaban CBN irin tasirin da sauyin kuɗin Najeriya zai yi ga zaɓen.
Shugaban na INEC ya buƙaci babban bankin da ya sauya wasu tsare-tsare musamman ma kan batun ƙayyade kudin da za a iya cirewa a duk rana domin a samu kuɗin da za a yi amfani da su a wasu ayyuka waɗanda ba za a samu damar tura su ta intanet ba.
Ya bayyana cewa akwai wasu ayyuka musamman masu motocin haya waɗanda dole da kuɗi lakadan za a biya su, kuma ya bayyana cewa saboda daɗewa a wannan aikin na zaɓe sun ga abubuwa iri-iri inda ya ce ana samun buƙatu na gaggawa a ranakun zaɓe inda hukumar ke buƙatar amfani da kuɗi.