Magunguna

Yadda Zaki Kawar Da Saukaken Tunbinki Koda Yakai Shekara 40

YADDA ZAKI KAWAR DA GIRMAN TUMBI

Tunbi dai yakan zowa mutum ta hanyoyi da yawa wanda kuma mafiya yawan mata basu fiya son su gansu da tunbi ba kai harma mazan basa bukatar sa.

Wannan hadi da zamu bayar yanzu insha Allahu indai kunyi amfani dashi to koda kunkai shekara arbain 40 dashi zai sauka.

ABUBUWAN DA ZAKU BUKATA.

• Cucumber 1.

• Lemon Tsami Guda 4.

• Ganyen Mint kamar Goma.

• Danyar citta.

• Ruwa kamar kofi 2.

YADDA ZAKU HADA:

Dafarko zaki yayanka cucumabrki sala-sala saiki samu abu mai tsafata ki zuba ki ajiye a gefe.

Saiki dauko lemon tsami guda 1 daga cikin 4 din da kika tanada zaki yayanka sala-sala saiki samu abu mai tsafata ki zuba ki ajiye a gefe.

Saiki dakko Danyar Cittarki ki bare fatar jikinta sai ita ki yanka ta sala -sala ki ajiye a gefe.

Sai ganyen mint naki guda goma shima ki gyra shi ki ajiyeshi mai kyau a gefenki

Abu nagaba saiki kawo ragowar ukun 3 lemin tsamin da kika ajiye saiki matse ruwansu a kofi mai kyau shima ki ajiye a gefe.

YADDA ZAKIYI DASU

Saiki kawo kofi mai kyau saiki zuba ruwan ki kamar kofi 2 saiki zuba yankakkun Lemon Tsami, Cucumber, Danyar Citta da kuma ganyen Mint a cikin wannan kofi da kuka zuba ruwan.

Saiku kawo wannan ruwan lemon tsami da kuka matse saiku zuba a cikin wannan kofi saiku juya sosai. Saiku sanyashi a masuburbudar sanyi yayi sanyi saku dinga shansa a kullum bashida wata matsala kuma zai kawar muku da wannan matsala cikin kankanin lokaci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu