Amfanin Tsamiya Ga Lafiyar Jikin Dan Adam
Tsamiya dai dan wani itace ne da take da matukar tsamin gaske, Tsamiya dai akan samunta a wurare dayawa cikin fadin duniyar nan.
Haka kuma mutanan da can kanyi amfani da tsamiya wajen magance cututtuka daban daban dake jikin dan Adam, amma kasancewar zamani yazo mana da wani tsari mu mutanan yanzu bamu damu da amfaninta ga lafiyarmu ba.
Wannan dalili yasa Shafin AlummarHausa yayi bincike don kawo muku wasu amfani da ita tsamiyar kanyi ga lafiyar jikinmu.
Da farko dai zaa nemi,
• Tsamiya,
• Zuma.
Yadda Za’a Sarfata.
Bayan kunsamu tsamiyaku masu kyau, saiku bare bawonta. Saiku jikata ta jiku sosai saiku tace ruwan tsamiyar a wani kofi mai kyau.
Bayan kun tace saiku kawo Zuma dinku mai kyau kadan saiku zuba a ciki ku juya sosai ta juyu.
Zaku dinga sha kullum safe da yamma kofi daya.
Kuma zatayi muku magunguna kamar haka;
• Yana Sanya Narkewar Abinci a cikin mutum da wuri.
• Yana Rage Kiba.
• Tana kawar da Cutar daji.
• Tana taimakawa Zuciya wajen gudanar da aiki.
• Tana taimakwa wajen warkar da rauni.
• Tana taimakawa fata wajen sanya haske.
• Tana taimakawa hanta wajen kareta daga samuwar cututtuka.
• Tana taimakawa masu gyambon ciki (Olsa).
• Tana maganin tari da kuma rage cutar Asma.
Alhamdulillah muna fata zaayi amfani da wannan hadi kuma a turawa yan uwa.