Magunguna

Amfanin Ayaba 12 A Jikin Ɗan Adam

AMFANIN AYABA A JIKIN DAN ADAM

  1. Ayaba takan taimaka yadda ciki zai sami sauqi wajen narka abin da aka ci don ta qunshi Starch wadda ake samu a cikin Carbohydrates, ba shakka yakan taimaka wajen rage qiba, ta yadda jikkuna za su fara diban wannan starch din a hankali, a sannan mutum zai riqa jin cewa ya qoshi, sai ya rage gabzar abincin.
  2. Ayaba takan sassautar da hauhawar jini, don tana da Potassium, shi kuwa yana da mahimmanci wajen wannan aikin.
  3. Zai yi kyau mutum ya sanya Ayaba a matsayin dan abin da zai riqa jefawa a baki lokaci zuwa lokaci kafin cin abinci, ya fi mutum ya ci abin da zai qara masa qiba, idan ya ji wata ‘yar kasala sai ya janyo guda ya kada ta a baki ya laqaqe ta, ta ma fi wasu juice din da suke dauke da Caffeine, masamman yadda ba ta da sukari sosai don dacewa da ci lokaci-lokaci, kamar in mutum yana wajen aiki, ko tarurrukan da kan dauki dogon lokaci, ko ma kallon talabijin.
  4. Ayaba takan kusan zama wajibi ko don lafiyar hanji, Ayaba qwara daya tal za ta iya yi wa matum maganin basir, don tana da wani nau’in Fibres na masamman wanda yake taimaka wa hanji wurin aikinsa, wannan magani halittacce ya fi qara lafiya sama da magungunan Bature, masamman wadan da suke da side effect.
  5. Banda wannan kuma Ayaba takan sanya kwanciyar hankali da dadin rai, domin tana da sinadarin Tryptophane wanda daya ne daga cikin sinadarorin da suke natsar da mutum da ba shi kwanciyar hankali na haqiqa, ta daidaita tsarin Protein a jiki, don ba wa mutum cikakkiyar sakewa.
  6. In da a ce mutum zai riqa cin Ayaba sau uku a rana, wato wajen kari da wurin kalacin rana ko na maraice to Potassium din dake cikinta zai qarfafa qwaqwalwarsa, don dalibai kuwa yakan fi amfani don yakan qara musu concentration sosai a lokacin daukar darasi.
  7. Game da mata masu ciki kuwa Ayabar takan taimaka don tana da fa’ida ba qarama ba ga mai juna biyu, masamman lokacin da take jin laulayi ko tashin zuciya wanda yake yawan faruwa in cikin yana qarami, sannan Ayabar za ta iya taimaka musu wajen ganin Glucose dake cikin jininsu bai nemi qaruwa ba, takan kuma lura da yanayin zafin jiki.
  8. Sai kuma zancen cizon sauro, wani in sauro ya cije shi sai ka ga wurin ya yi hulu-hulu, to a irin wannan yanayin za a iya bare Ayaba a sanya bawon a wurin, don yakan magance qaiqayin da wurin yakan yi, shi ma wannan ya fi aminci sama da magungunan da mutum zai yi tashafawa.
  9. Ayaba takan taimaka kuma wajen magance Ulcer, ko kuma riga-kafin hakan, domin takan taimaka wajen qanqanta Acid din da abinci yakan bari a tumbi, tawajen daidai acids din narka abincin, da wannan sai ka ga ta yi maganin matsalolin tumbi da dama.
  10. Ayaba tana da Iron sosan gaske ga wadan da suke da cutar fatarar jini ko Anaemia, don Iron din kan taimaka masamman ga qwayoyin jan jini wanda yake kula da dauko Oxygen, ya kuma tabbatar da cewa ruwan jiki wato white blood ya ba da gudummuwarsa wajen magance raunuka.
  11. Wani abin mamaki Ayaba hatta a gona bawonta yana da amfani, don kuwa takan zama taki idan aka kai ta can, kenan a maimakon a riqa zubarwa gwara a kai shi can inda za a yi aiki da shi don abincin da za mu ci.
  12. Ayaba takan taimaka sosai wajen kiyaye lafiyar qoda, ta yadda take qanqanta tura Calcium zuwa fitsari, da qaranta yuwuwar kamuwa da tsakuwar qoda, kamar yadda bincike ya gano cewa cin Ayaba yakan rage hatsarin kamuwa da kansar qoda, ta yadda aka sami mata wadan da suke cin Ayaba sau 4-6 a sati yadda suka nesanta da kamuwa da kansar qoda sama da wadan da ba sa ci, ban da wannan ma sinadarori masu dama da suke cikin Ayaba sun sanya tana iya kawar da matsalar Ulcer kai tsaye.

Galibin Ayaba har da karkasuwar nau’o’inta duk tana dauke da sinadarori kala daban-daban, akwai ma doguwar Ayaba wace yawancinta Inyamurai muke ganin suna sayar da ita, ba a iya cinta sai an soya, ko kuma a gasa ta a wuta, mukan ga ana sanya ta ne a abinci kamar shinkafa, sai a yanyanka ta a dora ta a sama, sunanta Plantain, sukan kira ta da Larabci “Mauzul Janna” ita wannan Ayaba tana da starch sosan gaske, kuma ba ta da sukari mai dama, ita ma tana da tasiri wajen kawar da maiqo a cikin jini, a taqaice dai ita ma ayaba ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu