Magunguna

Fa’idojin Auren Bazawara Ko Wacce Ta Girmeka A Shekarune

Fa’idojin Auren Bazawara Ko Wacce Ta Girmeka A Shekarune

ZAMANTAKEWAR AURE GA MA’AURATA:

Yana daga wasu fa’idoji da namiji zai samu in ya auri matar data girmeshi ko bazawara kamar haka.

☛ Nafarko zai sami ladan sunna biyu wato sunnar aure da kuma ta koyi da Annabin rahama S.A.W ya auri wacce ta girmeshe, musamman ma in ya yi dan koyi da fiyayyen halitta S.A.W.

☛ Auren mace wacce tafika shekaru akwai yuyuwar samun ingantacciyar ra’yuwar aure matukar akwai soyayya, sakamakon cewa ita ta zauna dawasu mazan tasan rayuwar aure, tasan mai namiji yakeso tasan maye baya so tasami kwarancewar iya kwanciya da miji saboda haka da zarar ka auri irin wan nan kuma akwai so dakauna da tarbiyya to ba ma auren da yafi shi dadi, sakamakon tasami working expereence koda bata taba aure ba a baya shekarun data yi a

rayuwarta zai sa taga abubuwa kala-kala a rayuwarta wadanda zasu zame mata darasi a zamantakewar aure nan gaba.
Haqiqa bazawara tafi budurwa sanin makamar aiki a zamantakewar aure musamman ma in ta sami saurayi wato wanda ta girma musamman ma ace akwai soyayya.

☛ Bazawara tana da hakurin zaman takewa fiye da budurwa dan ita tasan yau da kullum a aikace bawai abaka ba dan tagani akan wasu tagani akan kanta, sabanin budurwa ita kawai tagani akan wasune kawai.

da budurwa dan ita tasan yau da kullum a aikace bawai abaka ba dan tagani akan wasu tagani akan kanta, sabanin budurwa ita kawai tagani akan wasune kawai.

☛ Bazawara ko wacce tafika shekaru tarigaya tasan halayen iyayan miji da yadda ake zama da su sabanin budurwa.

☛ Ayyukan gida da kula da gida gyaran daki ,iya girki da tsaftace shi, kula da yara da sauran su dukkan su zawarawa sunfi ‘yan mata kwarewa a kai.

☛ Daddadan kalamai da kisisina da iya rarrashin miji, rashin katobara yayin zance, dadin shira dukka zawarawa sun kwarance fiye da ‘yan mata.

☛ Rashin almabazzaranci da dukiyar maigida, kamar bata abinci wasa da shi da sauransu.

Allah ka Azurtamu da mata na gari
Suma mata Allah ka Azurtasu da maza na gari
Albarkacin Annabi SAWW Amin yarabbi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu