AMFANIN KITSEN RAQUMI GA DAN ADAM
KITSEN RAQUMI WATO شھم الإبل
Shi dai Rakumi wata halitta ce ta ubangiji mai albarka domin albarkar da ubangiji madaukakin sarki yayi mashi yasa idan ya kasance yana tafiya cikin daji bishiyoyi nayi mashi kirari suna kiranshi zuwa gare su domin yazo ya yagi ganyen jikinta yaci ta samu wasu sinadarai daga yawunshi wanda sanadiyar cin wannan bishiya ita kuma wacce aka yagi ganyen nata ta kanzama wata hamsakiyar mawadaciya cikin yan’uwanta ta haka ne zata dinga raba ma dukkan yan’uwanta bishiyoyi wannan sinadarin ta karkashin kasa.
Yana da kyau kusani shifa rakumi dukkan jikin shi ko ina akwai magunguna a tare da dukkanin jikin nashi.
KAMA DAGA
•Fitsarin shi,
•Nonon shi,
•Kashin sa da Kitsen shi.
•Hantar shi da tumbin shi da dai sauran jikin shi baki daya.
To kamar Yanda Nafadi Zanyi bayani ne akan Kitsen Rakumi.
Shi dai Kitsen Rakumi yana magance miyagun cututtuka da yake lalata fatar jikin mutum.
Ana iya shafa kitsen Rakumi akan matsalolin fata kamar haka.
1-Kuraje
2-Makero
3-Kyasfi
4-Tautau
5-Faso
6-Gyambo
7-Kumburi
8-Kari
YADDA ZAAYI DASHI
Ga masu irin wannan matsalolin zasu wanke wajen da ruwan khal sai su shafa kitsen rakumi sau biyu a rana a inda matsalar yake tsawon kwanaki 9 za’a dace da yardan Allah.