Magunguna

Wasu Daga Cikin Amfanin Tazargade Ga Lafiyar Jikin Dan Adam.

Tazargade tana daya daga cikin dadaddun ciyawoyin da ake amfani da su a bangarori mabambanta na kiwon lafiya, kuma ana sanyata a ruwan wanki domin fitar da karni ko wari da dai sauran su.

Yanzu insha ALLAH za mu kawo muku wasu daga cikin amfanin da takeyi ga lafiyar mu, daga cikin abubuwan da take magancewa da yardar Allah su ne kamar haka:

1- Zazzabin cizon sauro, ko duk wani zazzabi na (Maleria).

2- Yawan ji da yin Amai

3- Masu matsalar Cutukkan da ke samun hanji, ko ciwon ciki.

4- Masu matsalar ciwon shanyewar barin jiki.

5- Mau matsalar ciwon Qoda

6- Tana daidata jinin al’ada.

7- Idan aka sanyata a ruwa aka karanta Ayoyin Alqur’ani aka sha kuma ana wanka da shi, tana magance matsalar Sihiri, Kambun-baka, Mayu, hassada da Shafar Shedanun Aljanu. Da yardar Allah.

8- Idan jinin al’adar mace baizo ba na tsawon lokaci, idan tayi amfani da Tazargade insha ALLAH zaizo.

9- Tana magance ciwon kan yara da kuma zazzaɓin yara, idan aka sanyata a ruwa ( normal mara zafi) akayi musu wanka da ita. Da yardar Allah.

YADDA AKE AMFANI DA ITA:

Ana dafata ne kamar yadda ake dafa shayi ( Tea) a sanya zuma ko sukari ( amma mai fama da ciwon Diabetics ba sai ya sa komai ba a haka zaisha), sai a rika shanta da dumi kamar shayi safe da yamma.

SHIN KOWA NE ZAI IYA SHA?

Eh kowa zai iya sha amma banda wadan nan:

1- Mai ciki ( Don zata iya haifar mata da matsalar lalacewar cikin ko da kuwa ya kai wata nawa).

2- Mai shayarwa
3- Mai ciwon farfadiya
4- Sai ƙananan yaran da basu wuce Shekarau 2 ba.

SHANTA YANA DA IYAKA NE ?

Eh ana so mutum yarika shanta a ko da yaushe amma kar ya kuskura ya haura sati 4 yana shanta a jere. ALLAHU A’ALAM.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu