Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Abba El-Mustapha

SUNA: Abba El-Mustapha
SANA’A: Fim
JINSI: Namiji
KASA: Najeriya
WURIN HAIHUWARSA: Jahar Kano,
YARE : Hausa
Yana da Arzikin da yakai $9 miliyan

Abba El-Mustapha jarumi ne kuma furodusa a masana’antar fina-finan Hausa. An haife shi ne a ranar 21 ga Janairu, 1978 a Unguwar Dandago, karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano, Najeriya. Abba El-Mustapha ya halarci makarantar Buk Staff School inda ya yi karatun firamare a shekarar 1984-1989. Sannan ya tafi makarantar gidauniyar jihar kano a makarantar sakandire 1989_1992. Sannan ya halarci makarantar sakandare ta alhassan usman kano, inda ya samu shaidar kammala karatunsa a shekarar 1995.
Jarumin ya karanci Gudanarwa, Rigakafin da Kula da Laifuka. Daga nan ya koma Kano State Polytechnic, inda ya yi digiri na biyu a fannin banki da kudi.

Sana’arsa

Abba El-Mustapha ya fara aikin wasan kwaikwayo ne a shekarar 2002, kuma bayan kammala karatunsa na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano, ya shiga harkar fina-finan Hausa, inda a halin yanzu ya kasance jarumi kuma furodusa. Ya shirya fina-finai da dama da suka hada da ruda, qamshi, dausayi, girma, feshi da jarumai. Ya kuma shirya fina-finai da dama sannan kuma ya yi tauraro a cikin fina-finai sama da 100.

Hakika Abba El Mustapha yana daya daga cikin jiga-jigan jaruman Kannywood da suka yi fice masu inganci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu