Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Alan Waka

An haife ni a shekarar 1973, a Unguwar Yakasai, a cikin ƙwaryar birnin Kano. Na yi makarantar firamare ta Tudun Murtala a 1980 zuwa 1986. Daga nan na yi makarantar sakandaren gwamnati ta Dakatar Kawaji, inda na kammala a shekarar 1992.

A nan ne na samu tsaiko, wanda ya ba ni ikon shiga fannin rubuce-rubuce na ƙirƙira, wato ƙagaggun labarai, domin a baya can akwai ƙagaggun littatafan Hausa da ake rubutawa na adabi kafin bayyanar fina-finan Hausa waɗanɗa da su ake yin wasan kwaikwayo.

A wanccan lokacin, da littatafan Hausa na ƙagaggun labarai al’umar Hausawa ke samun nishaɗi, ilimtarwa tare da ɗebe masu kewa. Su Malam Mamman da kasimu Yero ne ke gabatar da wasannin kwaikwayon a kafafen sadarwa na wancan lokacin.

Sai ni ma na samu kaina a matsayin mai ba da gudunmawa a wannan fannin, a lokacin na rubuta littafina na farko mai suna ‘Jirgi daya Ke dauke Da Ni.’ Sai littafina na ƙarshe mai suna ‘Ceto Ko Cuta?’ wanda Hukumar A Daidaita Sahu ta ɗauki nauyin bugawa.

Daga nan ban sake rubuta wani littafi ba har ya zuwa yanzu. Wannan harka ta rubuce-rubucen ne ta ba ni jinkirin komawa ga karatu sai a shekarar 2000 na koma Makarantar Kimiyya Da Fasaha ta Kano, a Unguwar Matan Fada, na yi karatun diploma a tsangayar zayyanar masana’antu.

Daga nan ne kuma na tsunduma a harkokin waƙe ta sigar zamani, inda muka buɗe masana’anta ta waƙa mai suna Hikima Multi Media, wadda take a kan Titin Gidan Zoo a Kano.

Wannan masana’anta, baya ga waƙoƙi muna yin ayyukan da suka shafi fina-finai da ɗab’i da bayar da hayar kayan sauti da sauran abubuwan da suka shafi sadarwa.

malamin na san su kuma shi ne ya ɗaura ni a cikin sha’ani na sha’awar bincike. Don haka a duk inda ka gan ni sai ka ga littafi a tare da ni ko ba zan karanta ba, domin masana sun ce al’ummar da take karatu ba daidai take da wacce ba ta karatu ba.

Don haka mutumin da yake yawaita bincike a kullum, ƙwaƙwalwarsa buɗewa take, tana ƙara ginuwa bisa tafarki na nazari da ilimi; yadda ko magana ya yi za ka ga tana cike da ilimi. Ni ma na yi dace da masana da suka ɗora ni a kan wannan tafarki.

Baya ga haka akwai kungiyar Marubuta Ta kasa (ANA), wacce take da reshe a Jihar Kano. Lokacin da na shiga ƙungiyar akwai zaman karatun da suke kira ‘Reading Seesion’ wanda sau ɗaya ake yi a wata.

A nan ne wasu ke karanta waƙoƙin tsunbure na Turanci ko ƙagaggun labarai. Bayan da na yi sabo da mambobin ƙungiyar sai ni ma nake zuwa ina karanta waƙa ta Hausa.

Ni ne mutum ɗaya da nake karanta waƙen Hausa a wannan lokacin, har sai da na yi shekara biyu ina yin haka.

A nan ne na sami gogewa ta rashin karkarwar murya a taron jama’a, domin na fi gwanancewa na yi waƙa da ka da baki ba kiɗa ba. A nan ne na iya fuskantar taron jama’a ina waƙa.

Akwai ɗalibai da malaman ilimi na Jami’ar Bayero, waɗanda in na gama za su yi mini tambayoyi da gyara. A ce na yi Ingausa a nan, a can ba haka ya kamata ka yi ba, can ka burge ni.

Sai da na yi wata 24 a haka ba tare da na yi fashi ba. A nan ne na samu gogewa da ƙwarewar da ake buƙata, a haka ne har na kawo inda nake a yanzu. Na zama Alan Waƙa, mutane kuma ke ganin ina wakiltar harshensu na Hausa a wurin isar da saƙo; domin da an ji waƙata za a san Bahaushe ne ke Magana.

Koda ko na sanya kayan kiɗa na zamani amma sautinsu yana ba da sautin Bahaushe ne, domin akwai dundufa a ciki, akwai duma da goge da kakaki, duk za ka ji irin kiɗan da ke wakiltar al’adun Hausa ne a waƙena, duk da cewa kayan kiɗan zamani nake sarrafawa.

Ko zaka yi mana ƙarin haske a kan adadin littattafan da ka rubuta zuwa yanzu?

Na rubuta kimanin littattafai guda tara kamar yadda na ambaci na farko da na ƙarshe. Shi littafina mai suna ‘Ceto Ko Cuta?’ yana magana ne a kan rashawa.

wato wani mutum ya ba ka wani abu don ka yi masa wata alfarna, ta yadda in bai ba ka ba; ba za ka yi masa alfarmar ba. Shin taimakonsa ka yi ko cutarsa ka yi? Wannan shi ne abin da littafin ya ƙunsa, domin ita rashawa ta bambanta da cin hanci kuma ita ce ummulhaba’isin kowace irin fitina.

Shi ne za ka ga da an ba wani muƙami mutane suna zuwa wajensa suna yi masa hidima, suna ba shi kyauta yadda wannan ne zai hana shi gudanar da aikinsa, ta yadda ya dace.

A haka duk inda ka bi za ka ga rashawa ta cuɗanya a harkokinmu na yau da gobe, tana sauya tunanin ɗan Adam, ta kashe zuciyarsa, ta sanya masa rashin tunani da ƙwazo.

Don haka na rubuta wannan ɗan ƙaramin littafi a kan haka, na rubuta waɗannan littattafai kimanin shekaru 15 da suka gabata. A cikin littattafan da na rubuta akwai ‘Cin Zarafi,’ ‘Baƙar Aniya,’ ‘Sawaba,’ ‘Cin Fuska’ da ‘Jirwaye’ sai kuma ‘Tarzoma.’

Ko me ya sanya salon waƙenka karɓuwa a wajan masu sauraro, musanman ɗalibai da malaman ilimin adabin Hausa?

Ni mawaƙi ne kuma makaɗin jama’a, Allah bai taƙaita ni da wani sashe kawai ba, don yin haka taƙaita fasaha ne. Kuma salon waƙena ya yi daidai da al’adar waƙar Bahaushe, domin ita waƙar Hausa kamar magana take, ba ta da bambanci da magana, ba kuma ta buƙar yawan raye-raye ko kaɗe-kaɗe mai tsanani. Da zarar an yi haka za ta zamo ba waƙar Bahaushe ba.

mungode da ziyara manuniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu