Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Amal Umar

Amal Umar (an haife ta a ranar 21 ga watan Octoban shekarar 1998) a Jihar Katsina, Nigeria ta kasance yar wasan kwaikwayo na Kannywood. Ta kuma fito a cikin shirin turanci na Nollywood MTV Shuga Naija tare da sauran taurarin Hausa, Rahama Sadau da Yakubu Muhammed.

Kuruciya da Ilimi

An haifi Amal a ranar 21 ga watan Oktoba shekarar 1998 a jihar Katsina, Najeriya. Tayi karatun ta na firamare da sakandare a Katsina, sannan ta koma jihar Kano domin yin karatun gaba da sakandare a Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano.

Sana’a

Amal Umar ta fara wasan kwaikwayo ne a shekara ta 2015, inda ta shiga masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood. Amma kafin ta fito a fim ta fara fitowa cikin bidiyon waƙoƙi tare da mawaƙa kamar Umar M Sherrif, Garzali Miko da sauransu. Ta fara fitowa a fim ɗin Hausa mai suna “Itikam” tun daga nan ta fara samun suna a faɗin ƙasar Hausa. Ayyukanta sun fara haskakawa bayan fitowarta ta farko a cikin jerin matasan Nollywood MTV Shuga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu