Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Jaruma Hadiza Gabon

Hadiza Aliyu an fi saninta da Hadiza Gabon (An haife ta a ranar ɗaya ga watan Yunin shekara ta 1989) a ƙasar Gabon,Hadiza Aliyu ta kasance shahararriyar ‘yar wasan kwaikwayo ce a Hausa film a Najeriya, a ƙarƙashin masana’antar fim ta Kannywood.

Farkon Rayuwa

An haifi Hadiza Aliyu Gabon ne a ƙasar Libreville da ke ƙasar Gabon, ta dawo Najeriya daga bisani domin wasu dalilai, inda tayo karatu, sannan ta fara harkan fim, Haifaffiyar garin Libreville, Jamhuriyar Gabon,[2] Hadiza Aliyu ‘yar gidan Malam Aliyu ne wanda dattijo ne. A ɓangaren mahaifinta, Hadiza ‘yar asalin ƙasar Gabon ce, kuma a bangaren mahaifiyarta, asalin ta Fulani ce daga jihar Adamawa, Najeriya.

Ilimi aduniya

Hadiza Aliyu ta halarci makarantun firamare da sakandiri a ƙasar haihuwarta inda ta rubuta jarabawarta ta A-Level tare da burin zama lauya sannan daga baya ta zabi Lauya a matsayin kwas din da ta fi so.

Ta fara karatun jami’a a matsayinta na daliba, amma dole ta daina zuwa makaranta saboda wasu matsaloli da suka dabaibaye karatunta. Karatun nata ya tsaya a lokacin kuma hakan ya ba ta damar halartar shirin difloma a cikin Harshen Faransanci kuma daga baya ta zama malama mai koyar da Faransanci a wata makarantar sirri.

Shahara a duniya

Tana daya daga cikin manyan jarumai mata a masana’antar fim ta kannywood.

Fim

Hadiza Aliyu ta shiga Kannywood ba da dadewa ba bayan ta shigo daga Gabon zuwa jihar Adamawa, Najeriya . Ta tashi daga Adamawa zuwa Kaduna yayin da take sha’awar shiga masana’antar fim ta kannywood tare da dan uwan ta.

Ta samu damar ganawa da Ali Nuhu kuma ta nemi taimakonsa don kaddamar da ita a matsayin ‘yar fim. Hadiza ta fara fitowa ne a shekarar 2009, inda aka sanya ta a Artabu, ta samu shiga masana’antar fim ta kannywood a matsayin daya daga cikin manyan jarumai mata tare da taimakon Ali Nuhu.

Da kuma jagorancin Aminu Shariff . Ta kasance shahararriyar ‘yar wasan Hausa ce Mutane da dama na gani da daukan ta a matsayin jarumar ‘yar wasan Kannywood kuma abar koyi musamman yadda take fitowa cikin sutura na al’ada da kyau.

Hadiza ta kasance ita ce jakadiyar da ta daga cikin kamfanin sadarwa na Najeriya MTN Nigeria da kuma kamfanin abincin Indomie, ta karbi kyautar Best Actress Jury Award a 2nd Kannywood Award wanda kamfanin MTN Najeriya suka dauki nauyin bayarwa. Ita ce wacce ta kafa gidauniyar HAG Foundation.

Hadiza ta yanke shawarar shiga Nollywood a shekarar 2017, biyo bayan Ali Nuhu, Sani Musa Danja, Yakubu Muhammed, Maryam Booth da Rahama Sadau .

An saka ta a fim dinta na farko na Nollywood kusa da Mike Ezuruonye, Mike Angel da Emmanuella a fim mai taken Lagos Real Fake Life .

Jakadanci

A watan Disambar 2018 ne, kamfanin NASCON Allied Plc, wanda ke reshen rukunin kamfanonin Dangote ya bayyana Hadiza Aliyu a matsayin jakadiyar jakadancin Dangote Classic Seasoning a yayin kaddamar da kayan.

Taimako

A shekara ta 2016, Hadiza ta kafa ƙungiyar agaji mai suna HAG Foundation Da nufin inganta rayuwar talakawa ta hanyar samar da taimako a bangarorin ilimi da kiwon lafiya gami da wadatar abinci. Ta zama daya daga cikin ‘yan wasa mata na farko a tarihin Kannywood da ta gabatar da irin wannan taimakon jin kai.

A watan Maris na shekara ta 2016, ta ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijirar da ke cikin jihar Kano inda ta ba da gudummawar kayayyakin abinci, kayan masaka da sauran kayan masarufi da mazauna sansanin suke bukata saboda rikicin arewacin Najeriya.

Lamban girma

Hadiza Aliyu ta samu kyaututtuka da girmamawa da dama wadanda suka hada da 2013 Best of Nollywood Awards da 2nd Kannywood / MTN Awards a 2014. Saboda karramawar da ta yi a matsayin ‘yar fim, Hadiza ta karrama a shekarar 2013 daga tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso . An kuma ba ta lambar yabo ta Hollywood ta Afirka a matsayin Jarumar Jarumai.

  • Fina finan ta
  • Shekara Sunan Fim Matsayin Nau’i
  • Daina Kuka Jaruma Fim
  • Farar Saka Jaruma Fim
  • Fataken Dare Jaruma Fim
  • Kolo Jaruma Fim
  • Mukaddari Jaruma Fim
  • Sakayya Jaruma Fim
  • Umarnin Uwa Jaruma Fim
  • Ziyadat Jaruma Fim
  • 2009 Artabu Jaruma Fim
  • 2010 Wasila Jaruma Fim
  • 2010 Umarnin Uwa Jaruma Fim
  • 2012 Aisha Humaira Jaruma Fim
  • 2012 ‘Yar Maye Jaruma Fim
  • 2012 Badi Ba Rai Jaruma Fim
  • 2012 Akirizzaman Jaruma Fim
  • 2012 Dare Daya Jaruma Fim
  • 2012 Wata Tafi Wata Jaruma Fim
  • 2013 Da Kai Zan Gana Jaruma Fim
  • 2013 Haske Jaruma Fim
  • 2013 Ban Sani Ba Jaruma Fim
  • 2014 Mai Dalilin Aure Jaruma Fim
  • 2014 Daga Ni Sai Ke Jaruma Fim
  • 2014 Ali Yaga Ali Jaruma Fim
  • 2014 Basaja Jaruma Fim
  • 2014 Uba Da ‘Da Jaruma Fim
  • 2014 Indon Kauye Jaruma Comedy/Fim
  • 2014 Ba’asi Jaruma Fim
  • 2014 Jarumta Jaruma Fim
  • 2017 Gida da waje Jaruma Fim
  • 2017 Ciki Da Raino Jaruma Comedy/Fim
  • 2019 Hawwa Kulu Jaruma Fim
  • 2019 Wakili Jaruma Fim
  • 2019 Dan Birnin Jaruma Fim
  • 2019 Gidan Badamasi Jaruma Comedy/Fim

Mungode da ziyarar mu domin samun ayyukanmu kuci gaba da kasancewa da shafinmu mai albarka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu