Magunguna

Alamomin Kambun Baka Da Kuma Hassada A Jikin Mutum Da Yadda Za’a Nemi Kariya.

1- Jin zafin jiki mai tsanani.


2- Mutum yaji ya rabu da yin ibada (Alhalin kuma a baya ba haka yake ba) kamar yin sallah akan lokaci, Karatun alqur’ani, Azkaar da sauran ibadu na farilla ko na nafila, duk sai yaji ba ya iya yinsu a yanzu.

3- Yawan bugun zuciya akai-akai.

4- Yawan yin bacci da yawa ba tare da wani dalili ba.

5- Zuciya ta rika shiga k’unci da yawan sauyawar yanayin halayyar mutum kamar ( mutum yaji nan da nan ya shiga wani hali na qunci) .

6- Jin tsoro da kuma yawan firgita

7- Yawan yin muggan mafarkai da na firgici.

8- Mutum yaga wasu cututtukan fata sun fito a fatar jikinsa wadanda za a rasa gane kansu.

9- Bayyanar kurajen pimples (marasa jin magani) a fuskar mutum.

Wadan nan wasu kenan daga cikin alamomin hassada a jikin mutum, ta yadda hakan yake cutar da muta inne har a rasa gane abinda ke damunsu, ayita zuwa asibiti amma lamarin shiru.

ABIN LURA

MAFITA

Mutum ya dage wajan kiyaye dokokin Allah sau da kafa, kuma mutum ya rika boyewa kuma yabar yayata ni’imominsa ko sirrukansa ga kowa musamman ma a social media, saboda komai na iya faruwa.

Mutum ya yawaita yin Azkaar musamman karanta Surorin nan : IKHLAS, FALAQI da NASI sau 3 da safe da yamma, sau 1 bayan kowacce sallar farilla amma bayan sallolin Asubahi da magriba sau 3 akeyi, idan akazo kwanciya bacci sai a hada tafin hannuwanka ka matso da su daf da bakinka tayadda iskar karatun za ta rika dukan tafin hannuwan, a karanta surorin sau 3 kuma a tofa sai a shafe jiki gaba daya.

Insha Allahu Allah zai kareka da kariyarSA, Allah yasa mudace.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button