Hanyoyin Da Zaabi Don Wanke Dattin Ciki
YADDA ZA’A WANKE DATTIN CIKI.
Kasancewa ciye-ciye da mukeyi a rayuwar mu ta yau da kullum, sautari mukan ci abinci da kayan kwalama iri-iri fiye da sauran halittun dake rayuwa a ban kasa. Ba wata halitta daya da take da ilmin sarrafa abinci da abin sha da sauran nau’ukan abinci kamar halittar Dan-adam. Mutum kan sarrafa abinci dangin kayan zaki kamar su:
• Biredi,
• Biskit,
• cin-cin,
• Fanke,
• Kunun zaki,
• juice,
• Cake
Dadai sauran kayan zaki na gwangwani na roba da kuma na kwalba.
Baya ga abinci dangin kayan maiko kamar irinsu :
- Kosai,
- Fanke,
- Dankali,
- Kwai,
Dadai sauran nau’ikan kayamci masu maiko.
Wadannan na daya daga cikin abubuwan dake taruwa a ciki su haifar da cinkoson kazanta domin ciki zai cushe da ababuwa daban daban ya kasance wata illa ga lafiyar ciki.
Hakan ka iya haifarda da cututtuka kmaar haka:
- Tashin zuciya,
- Kumburin ciki,
- Rashin iya cin abinci,
- Gajiya da Kasala
Dadai sauran wasu cututtuka.
Domin Magance Wannan Matsala ta dattin ciki sai a nemi.
• Lemun tsami
• Apple
• citta
YADDA ZA’A HADA
za’a tafasa ruwan zafi kamar Kofi daya madaidaici na glass sai a zuba cokali daya karami na garin ginger. Sai a matse lemun tsami daya a ciki. a zuba cokali daya babba na ruwan apple sannan a sha.