Siyasa

Peter Obi ya lashe kananan hukumomi 12 a jihar Edo, yayin da Tinubu ya ci shida

Jam’iyyar Labour ta samu nasara a kananan hukumomi 12 a jihar yayin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta lashe sauran kananan hukumomi shida da suka bar jam’iyyar PDP ba ta da karamar hukuma.

Da yake bayyana sakamakon zaben, jami’in tattara bayanai na jihar Edo, mataimakin shugaban jami’ar Uyo, Farfesa Nyaudoh Ndaeyo, ya ce dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi ya samu kuri’u 331,163 ya lashe zaben shugaban kasa a jihar.

Jam’iyyar LP ta samu kuri’u 331,163, APC na da kuri’u 144,471 yayin da PDP ta samu kuri’u 89,585 yayin da New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta samu kuri’u 2,743.

LP ta lashe zaben shugaban kasa a kananan hukumomi 12 na Igueben, Esan Central, Esan North-East, Egor, Esan South-East, Esan West, Uhunmwonde, Orhionmwon, Ovia South-West, Oredo, Ikpoba-Okha da Ovia North-East, a cikin Edo South da Edo Central.

APC ta samu nasara a kananan hukumomi shida na Owan West, Owan East, Akoko-Edo, Etsako Central, Etsako West da Etsako East, duk a gundumar Edo ta Arewa, inda tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole ya fito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button