Farashin abinci zai sauko a Najeriya nan da watan Satumba
DA DUMI-DUMI: Farashin abinci zai ragu a Najeriya nan da watan Satumba –Masana tattalin arziki sunyi hasashe
Daga Shafin A Yau
Babban jami’in kula da hada-hadar kudi, Bismarck Rewane ya ce ana sa ran farashin abinci a Najeriya zai ragu nan da watan Satumba mai zuwa,
Jaridar Manuniya ta ruwaito a cewar masanin ana hasashen farashin kayayyaki zai sauko daga kashi 34.19 zuwa tsakanin kashi 32 zuwa kashi 28,
Rewane, ya ƙara da cewa zuwan matatar Dangote wacce za ta soma fitar da mai daga watan Agusta, da kuma cire haraji wajen shigo da kayan abinci na kwanaki 150 da Gwamnati ta yi da kuma sabon mafi karancin albashi na N70,000 da aka zartar zai yi tasiri ga saukowar hauhawar farashin kayayyaki domin talakawa su samu sauƙi.
A Yau ta ruwaito a hirarsa da kafar Talbijin ata Channels masanin ya kuma kara da cewa ana hasashen hatta darajar Naira ita ma za ta yi tashin gwauron zabi idan aka kwatanta da Dala a kasuwar canji a watanni masu zuwa.