Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Zee Pretty

Zulaihat Ibarhim Zee Pretty na daya daga cikin Jaruman Shirya Finafinan Hausa dake Kano, kuma mai basira wajen yin rawa da kuma shirya gajerun finafinan Barkwanci.

An haifi Zulaihat Ibrahim da akafi kira da Zee Pretty a shekarar alib 1997, a Ruba karamar hukumar Dankuwa dake jihar Kebbi a Najeriya.

Zee Pretty tayi karatunta na Firamari da Sakandire a Jihar Kebbi, bayan kamala Sakandirenta sai ta tafi Federal College of Education dake jihar Sokoto, inda ta samu shaidar NCE.

Zee pretty bata tsaya iya nan ba taci gaba da karatunta zuwa Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, daga bisani kuma ta shiga masana’antar shirya finafinan Hausa.
Zee Pretty ta taso da matukar son zama daya daga cikin Jaruman Hausa fim tun tana karama kasancewar kallon finafinan Hausa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu