Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Zara Diamond

Rayuwar Jaruma Zara Diamond da Fara Fitowa a Film

Zahra Muhammad wacce aka fi sani da Diamond Zahra ko Zahra Buzuwa kwararriyar yar wasan Najeriya ce. An haifi Zahra a garin Tahoua amma ta yi karatun firamare da sakandare a Maradi. Ta fito daga kabilar Abzinawa.

Zahra ta koma Najeriya inda ta shiga masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood a shekarar 2018. Fim din da ya kawo shahararriyar jarumar shi ne fim din “Zuma Da Madaci (2018) Zarah ta fito a fina-finan Hausa daban-daban kamar su Hanan, Barista Kabeer, Gidan Sirikai. Sirrin So (Series), Yaudara, da dai sauransu, ta kuma fito a wakokin Hausa da dama tare da mawakan Hausa irinsu; Hamisu Breaker, Garzali Miko, Umar M Shariff da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu