Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Rukayya Dawayya

Rukayya Umar Dawaiya (an haife ta a ranar 17 ga watan Oktoba,a shekara ta alif 1985) ƴar wasan Kannywood ce daga jihar Kano a Najeriya .

Farkon Rayuwa da Ilimi

An haifi Rukayya Umar Dawayya ranar 17 ga watan Oktoba a shekara ta alif 1985 a Kano. Mahaifinta hamshaƙin ɗan kasuwa ne dan garin Matazu jihar Katsina kuma mahaifiyarta ‘yar jihar Borno ce . Dawayya ta yi Makarantun Firamare da Sakandare a Kano, ta samu takardar shaidar harshen Larabci a kasar Saudiyya. Dawayya ya kuma samu takardar shaidar kammala Diploma a Mass Communication a Jami’ar Bayero Kano.

Sana’a

Rukayya Umar Dawaiya ta fara fitowa a fim a shekarar 2000 a cikin fim dinta na farko mai suna “Dawayya” wanda ya sa aka ba ta sunan Dawayya. A shafinta na yanar gizo, ta bayyana cewa ta yi kaurin suna a cikin fim din Dawayya kuma ya kara mata kwarin gwiwar ci gaba da shirya fina-finai. Dawayya ta yi fina-finai sama da 150 a masana’antar fina-finan Hausa. Dawayya jakadi ne a wasu kamfanoni a ciki da wajen Najeriya. Ita ma ƴar siyasa ce kuma ‘yar kasuwa.

Rayuwa ta sirri

Dawayya ta yi aure a 2012 kuma ta rabu a 2014.[8] Tana da da wanda aka haifa a Makka Saudi Arabia.[9]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu