Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Momee Gombe

Takaitaccen Tarihin Jaruma Momee Gombe..

Maimuna Abubakar da akafi sani da (Momee Gombe), na daya daga cikin Jaruman masana’antar shirya finafinan Hausa dake Kano,  wanda tauraronta ya haska a shekarar 2020.

An haifi jaruma Maimuna Abubakar da akafi sani da Momee Gombe a garin Gombe dake Najeriya, a ranar 28 ga watan June a shekarar alib 1997. Tayi makarantar Firamari da Sakandire a garin na Gombe.

SHIGARTA MASANA’ANTAR FIM

Jarumar ta taso da sha’awar zama daya daga cikin Jaruman na finafinan Hausa dake Kano tun tana karama, harma take ganin babu wani fita a shirin fim wanda zai bata wahala.
Jarumar ta shiga masana’antar shirya finfinan Hausa dake Kano ta hanun babban Frodusa Usman Ma’azu a shekarar 2017, Kuma an fara haskata a fim dinta na farko mai suna ANGO

WAKOKINTA


Momee Gombe tayi wakoki da dama wanda sukakai 40 zuwa hamsin kuma tayi da manyan Jaruman Masana’antar shirya fim dake Kano kamar su;

Adama A Zango, 

Hamisu Breaker,

Garzali Miko dadai sauransu.

Momee Gombe ta bayyana dalilin samun Sunanta wato Momme  da cewa sunan kakarta ne “Maimuna” don haka iyayenta basa iya kiran sunan suke kiranta da “Momee”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu