Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Abubakar Bashir Mai Shadda

Abubakar Bashir Abdulkarim wanda aka fi sani da Abubakar Bashir Maishadda (an haife shi a ranar 2 ga watan Agusta na shekarar 1988) ya kasance furodusan finafinai ne wanda ke aiki a masana’antar fim ta kannywood. Shi ne shugaba kuma mamallakin kamfanin Maishadda Global Resources LTD.

Abubakar Bashir Maishadda ya shirya fina-finai da dama a karkashin tutarsa da ya kunshi manyan taurarin kannywood irin su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Maryam Yahaya, Yakubu Mohammed, Rahama Sadau a fina-finai kamar Takanas Ta Kano a shekara ta (2014), Daga Murna (2015), Wutar Kara (2019), Hafeez (2019), Mujadala (2019), Mariya (2019).

Ana Dara Ga Dare (2018) da Hauwa Kulu (2019), da sauran kamfanonin samarwa da yawa irin su Sareena a shekara ta (2019), da The Right Choice a shekara ta (2020), Abubakar Bashir Maishadda ana daukar shi a matsayin “gogan fasa tisi” saboda kudin da finafinan sa suke janyowa.

Abubakar Bashir Maishadda ya samu lambobin yabo da yawa ciki har da City People Entertainment Awards a shekara ta 2018 da shekara ta 2019, 2015 Africa Magic Viewers Choice Awards a rukunin mafi kyawun nau’in harsunan asali na (Hausa).

Finafinan daya shirya

 • Take Shekara
 • Binkice : 2014
 • Budurwa : 2014
 • Tarayya : 2014
 • Bakar Inuwa 2014
 • Sakaina : 2014
 • Farin Gani : 2014
 • Zee Zee : 2014
 • Hakkin Miji. : 2014
 • Munubiya : 2014
 • Da’ira : 2014
 • Kafin Safiya. : 2014
 • Gobarar Mata : 2014
 • Takanas Ta Kano : 2015
 • Dan Gaske : 2015
 • Mafiya : 2015
 • Daga Murna Anga Jaka : 2015
 • Kishiya Da Kishiya : 2015
 • Gidan Abinci : 2016
 • Kowa Darling : 2016
 • Karfen Nasara : 2016
 • Tsakar Gidan Jatau. : 2016
 • Kwamandan Mata : 2016
 • Kauyawa. : 2016
 • Mijin Aro : 2016
 • Biki Buduri 2016
 • Kanwar Dubarudu : 2016
 • Ruwa A Jallo : 2016
 • Burin Fatima 2016
 • Mubeena : 2016
 • Bashi Hanji : 2016
 • Dije Rama : 2016
 • Kalan Dangi : 2016
 • Mariya : 2018
 • Mujadala : 2018
 • Wannan ita ce Hanya : 2018
 • A Neman Sarki : 2018
 • Ana Dara Ga Dare : 2018
 • Sarkakiya : 2018
 • Hafeez : 2019
 • Sareena: 2019
 • Halimatus Sadiya : 2019
 • Nadiya 2019
 • Wutar Kara : 2019
 • Hauwa Kulu : 2019
 • Bana Bakwai : 2019
 • Ciwon Idanu Na : 2019
 • So Da So : 2019
 • Zabi Daidai : 2020
 • Bintu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu