Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Mansurah Isah

Mansura Isah tsohuwar ‘yar fim din Kannywood ce, kuma Darakta ce, an haifeta a ranar 25 ga Fabrairu, tana da kanwa mai suna Maryam Isah, wacce ita ma shahararriyar ‘yar fim din Kannywood ce. Mansura Isah kyakkyawa ce kuma yar baiwa, wacce ta fara aiki a matsayinta na shugabar bidiyo ta mata ta farko a Kannywood kafin ta tsunduma cikin wasan kwaikwayo a karshen shekarun 1990. Mansura ta bar wasan kwaikwayo dalilin aure, don ta zauna tare da mijinta. Mijinta shi ne Sani Musa Danja wanda shi ma shahararren dan wasan kwaikwayo ne. Sun yi aure a 2007 kuma aurensu ya samar da ‘ya’ya huɗu, Khadijatul Iman, Khalifa Sani, Yakubu da Yusuf. Mansura ta kasance ‘yar garin Kano ce.

Fim

Mansura ta taka rawa a finafinai da yawa kamar ‘Yan Mata da Gurnani da Jurumai da Zazzabi da Turaka da sauransu. Mansura Isah ita ce ta kirkiro gidauniyar ‘Toay’s Life Foundation’ sannan kuma ta fi mayar da hankali a kan rubuta fina-finai ga furodusoshi wadanda ke biyanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu