Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Hassan Giggs

Zantawa da jarumi mai ‘daukar hoto kuma mai bada umarni a fina finan Hausa Hassan Giggs wanda ya shafe shekaru 18 yan wannan sana’a.
Hassan yace ya fara wannan sana’a da tace hoto wato editing a turance tun shekara ta 1994, shekaru uku bayan fara wannan aiki ya koma mai ‘daukar hoto, ya kuma kara zuwa wasu makarantu akan harkar fim domin karin ilimi, wanda hakan yasa ya zama mai bada umarni. Har yanzu dai Hassan na ‘daukar hoto kuma yana bada umarni.
Sha’awa da son wannan harka ta fina finai itace dalilin sa yin wannan sana’a har ya zuwa yanzu, inda yace duk abinda baka da sha’awar sa to bazaka taba samun nasara kan abin ba, kasancewar sha’awar da yake yiwa shirin fina finai hakan ne yasa kullum yake tafiya da zamani, domin a duk lokacin da zamani yazo da sabon wani abu to shima zai tafi makaranta domin karowa kansa ilimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu