Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Sunusi Oscar 442

Sunusi Hafeez wanda aka fi sanida Sunusi Oscar 442 sanannen mai bada umarni ne a masana’antar Kannywood. Mai bada umarnin ya bayyana yadda ya shiga masana’antar Kannywood. Ya bayyana cewa, ya girma a garin Kano ne a karamar hukumar Fagge ta jihar. Ya kasanace mai son kallon dirama bayan ya tashi daga makaranta. daga nan ne ya fara son lamarin tare da shigewa masu shiryawa. A hakan ne kuma ya fara bayyana musu kurensu. Daga baya ya bawa wasu abokansa shawarar fara sana’ar fim amma kuma babu jari. Daga baya kuma ya samu kudin fara shirya fina-finansa na kansa.

Da aka tambayi daraktan yadda ya zama darakta bayan a furodusa kuma dan wasa ya fara a masana’antar, sai yace, “Tun farko ni inasson gyaran kure ko a lokacin. Duk abinda bai min ba nakan gyarashi. Toh daga nan ne na fara gwada sa’ata a fannin bada umarni. Shekaru 20kenan da suka shude. Tun daga nan kuwa na cigaba da bada umarni,” Oscar ya bayyaan burinsa na zama mai bada umarni a masana’antar Bollywood har da Nollywood. ya kuma tabbatar da cewa, ba zai sassauta ba wajen cika wannan burin nasa. baya fatan ya kammala aikinsa da masana’antar kannywood kadai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu