Tinubu Ya Yi Alkawarin Biyan Ma’aikatan Najeriya Albashi Mai Gwabi.
Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya tabbatar wa ma’aikatan Najeriya cewa, zai biya su mafi karancin albashi, walwala da kuma tabbatar da dai-daito.
Ya ba da wannan tabbacin ne a ranar Litinin a Abuja a sakonsa na hadin kai ga ma’aikatan Najeriya a ranar ma’aikata ta duniya ta 2023.
Ya kara da cewa ma’aikata a kasar nan za su samu albashin mai kyau, rayuwa mai kyau da kuma wadata iyalansu a karkashin shugabancinsa.
Tsohon gwamnan jihar Legas, ya kuma tabbatar wa ma’aikatan Najeriya cewa shi amintaccen amininsu ne kuma abokin aiki a fafutukar tabbatar da adalci a zamantakewa da tattalin arziki ga daukacin ‘yan Najeriya.
“Na bi sahun sauran kasashen duniya da sauran ‘yan kasa domin yin bikin ma’aikatan Najeriya a ranar ma’aikata ta duniya ta bana.
“A wannan rana ta musamman, a matsayina na zababben shugaban kasa, ina mika hannun abokantaka na ga ma’aikatan Najeriya ta hanyar kungiyoyin kwadagon tsakiya guda biyu – Nigerian Labour Congress (NLC) da Trade Union Congress (TUC).
“A cikina, za ku sami amintaccen abokin tarayya kuma abokin aiki a yakin neman adalci na zamantakewa da tattalin arziki ga daukacin ‘yan Najeriya, gami da duk ma’aikata.
“Yakinku zai zama yakina domin koyaushe zan yi muku adalci,” in ji Tinubu.
Ya ce tsare-tsaren sa na kyautata jin dadin rayuwa da kuma yanayin aiki ga ma’aikatan Najeriya an bayyana su karara a cikin manufofin sa ta Renewed Hope don inganta Najeriya.
Akarshe ya ce yaki da fatara, jahilci, cututtuka, rarrabuwar kawuna, kiyayyar kabilanci da addini da duk wani mummunan halu da ke fada da zaman lafiya da ci gaban kasar nan.
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta hana shigo da taliyar yara wanda aka fi sani da Indomie cikin kasar nan. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Darakta Janar na Hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana haka a wata hira da manema labarai a ranar Litinin.