Gwamnatin Tarayya Ta Yadda Da Samar Da Karin Jami’a A Garin Kano
Gwamnatin Tarayya Ta Yadda Da Samar Da Karin Jami’a A Garin Kano.
amince daukaka darajar kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso zuwa Jami’ar Ilimi.
Shugaban hukumar ta NUC, Farfesa Abubakar Rasheed, ya mikawa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano takardar NUC ta amincewa da mayarda kwalejin zuwa Jami’a ranar Talata a Abuja.
Shugaban na NUC ya ce jami’ar ita ce ta 61 mallakar gwamnati kuma ta 221 a daukacin tsarin jami’o’in Najeriya.
Farefesa Rasheed ya yabawa gwamna Ganduje bisa wannan shiri na kafa jami’ar, inda ya ce za ta taimaka matuka wajen biyan bukatun ilimi a jihar Kano.
Da yake jawabi tun da farko, Ganduje ya ce sabuwar jami’ar wadda ita ce ta uku da gwamnatin Kano ta mallaka, gwamnatinsa ce ta samar da ita domin biyan bukatun ilimi tare da samar da ma’aikata.
Ya ce, makarantar tana alfahari da malamai 116 da ke da digiri na uku.