Labarai

Buhari Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Shugaban Kasar UAE Bisa Rasuwar Surukarsa

Buhari Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Shugaban Kasar UAE Bisa Rasuwar Surukarsa.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aike da sakon ta’aziyya ga Shugaban kasar hadaddiyar daular Larabawa bisa rasuwar sirikarsa Sheikha Maryam Al Falasi.

Maryam Al Falasi ita ce mahaifiyar Sheikha Salama, matar shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan.

A cikin sakon da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya aike a ranar Alhamis, Buhari ya shaida wa shugaban na UAE, wanda ke matsayin Sarkin Abu Dhabi, cewa ya yi matukar bakin ciki da rasuwar surukarsa.

Buhari ya yabawa Sarkin bisa yadda yake rike da kyakkyawar alaka da gwamnati da al’ummar Najeriya.

Ta’aziyyar ‘yan Najeriya na tare da gwamnati da jama’ar UAE a wannan mawuyacin lokaci.

Kazalika yayi addu’ar Allah ya jikanta ya sa ranta ya huta cikin aljanna Firdausi,” in ji shugaban.NAN

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa ta cika alkawarin samar da sauyi wanda ta yiwa ‘yan Najeriya alkwari.

Idan za a iya tunawa, kafin zaben shugaban kasa na 2015, jam’iyyar APC, ta mayar da karfi kan samar da sauyi a lokacin yakin neman zaben ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button