Kwamishinoni 11 sun fice daga PDP Sun Koma APC a Sokoto yayin da ake kusa da Zabe.
Kwamishinoni 11 sun fice daga PDP Sun Koma APC a Sokoto yayin da ake kusa da Zabe.
Kimanin kwamishinoni goma sha daya ne a jihar Sokoto suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Wannan ci gaban ya biyo bayan sanarwar da mataimakin gwamnan jihar, Manir Muhammad Dan Iya ya yi na ficewa daga babbar jam’iyyar adawa.
MANUNIYA ta ruwaito cewa Muhammad ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Kware a karamar hukumar Kware a jihar.
Rahotannin sauya shekar sun shiga kafafen yada labarai sa’o’i kadan kafin gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki. Ana sa ran dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da abokin takararsa, Kashim Shettima, za su isa jihar domin gudanar da yakin neman zaben ranar Alhamis.
Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tarbi wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a lokacin gangamin.