Uncategorized

Kalli sana’o’in wasu jaruman kannywood kafin su shigo harkar film, abin zai baku mamaki

Zamu iya cewa kashi 90 cikin 100 ma jaruman kannywood akwai wata sana’ar da suke yi sannan suka samu damr shigar matsana’antar kannywood hakan yasa muka bincike muku wasu sana’o’i da wasu jaruman kannywood suka yi kamin su shigo matsana’antar film.


 
HADIZA GABON

Ta kasance daya daga cikin jaruman da suka sha wahala sosai kamin su samu daukaka a yadda ake ganin su a yanzu, yanzu dai ta kasance daya daga cikin manyan jaruman kannywood mata da suka fi kudi, jarumar haifaffiyar kasar gabon a baya ta kasance Malamar makaranta ce a kasar gabon daga bisa ni tabar karantarwar tazo kasar Nijeriya ta shigo masana’antar film ta kannywood.


 
MARYAM YAHAYA

Matashiyar jarumar kannywood da ta shigo matsana’antar ta kannywood a lokacin da take tashen balaga kuma ta shigo matsana’antar ne da kafar dama inda ta samu daukaka cikin kankanin lokaci, ita dai a baya kamin a fara sakata Film a lokacin da tazo kallon yan film, ta kasance tana saida awara a bakin kofar gidan su wanda da yawa daga cikin mutanen suka santa kamin ta fara harkar film suka shaida.


 
ADO GWANJA

Mawakin mata da a duniyar hausawan yanzu babu wani mawakin mata da ya kaishi, kamar yadda wani malami ya faɗa tunda yacewa mata ” sama ” har yanzu fa basu sauko ba.

Mawakin yayi suna ne a shekaru hudu da suka gabata bayan ya fito a film din dan kuka a matsayin wanda yake jan ragamar shirin, a wata hira da aka taba yi da shi ya tabbar da cewa shi sana’ar “shayi” yake kamin ya sunduma matsana’antar kannywood, kuma sana’ar shayin nan gabon gidan su ne, kamin mahaifinsa ya rasu har sarkin kano yana sawa a siyo masa shayi daga wajen su.


 
HAMISU BREAKER

Babban mawakin kannywood mamalankin wakar “Jaruma” da yayi sanadiyar haska shi a duniya, mawakin dai yanzu Allah ya sanya shi cikin manyan mawakin kannywood da suka yi kudi cikin kankanin lokaci a harkar waka,

dama shi waka haka yake idan kayo Sa’a kayi wata waka da ta sanu karbuwa sosai a wajen jama’a tofa sai muce ka karka ta yanke saka, shi dai mawakin kamin a sanshi a harkar waka sosai, ya bayyacewa cewa shi tela ne wato dinkin kaya yake.


 
DADDY HIKIMA

Daddy hikima wanda aka fi sani da abale, jarumi ne da ya saba fitowa a matsayin dan daba, dan shaye-shaye, mara imani da dai sauran su, duk wa’yannan halayen a finafinai kawai yake yin su, amma duk da haka wasu na ganin cewa haka halinsa yake ko a zahiri,

jarumin a wata hira da yayi da BBC hausa a shirin su na daga bakin mai ita ya bayyana cewa shi ya kasance nurse ne wato jami’in lafiya kamin ya ƙusa harkokin finafinai gadan-gadan amma duk da haka wasu ranaku yana kawo ziyara asibiti domin ya bada gudunmawar aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu