Cikakken Tarihin Fauziyya D Sulaiman
Fauziyya D. Sulaiman wadda aka fi sani da Matar Bello Q far Q an haife ta a unguwar Fagge a Shekarar 1981 ta yi karatuna na Firamare a Makarantar Festival Primary School, daga nan wuce makarantar ‘yammata ta kwana Government Girls Secondary School ‘Yar gaya a shekara ta 1993, bayan ta kammala karatunta na Jiniya ta koma Makarantar Government Girls College Dala ta karasa karatunta daga 1995 zuwa 1998. Daga nan ta yi aure a shekara ta 1999. A shekara ta 2003 ta koma karatu a Makarantar College of Health Sciences, School of Hygiene in da ta yi Diploma a kan Assistant Nutritionist. Daga nan ta yi Certificate a Makarantar School of Management, akan Hotel and Catering Services.
A game da rubutu kuwa ta fara rubuta littafi a shekarar 2002, in da littafi na farko mai suna Me na yi mata?. Daga nan ta ci gaba da rubuta littafi da suka hada da:
- Kishin Banza
- Guduna Ake yi
- Rayuwar ‘Ya Mace
- Mece ce Rayuwa
- Burin Raina
- Karshen Wahala
- Labarin Zuciya
- Matsalar Mace
- Mijin Uwa
- Auren Kudi
- Duk Abinda Namiji Ya yi
Fauziyya mamba ce a Kungiyar Marubuta ta Najeriya reshen jihar Kano kuma tana rike da mukamin jami’a a majalisar gudanarwa ta Kungiyar tun watan Maris na 2009 har zuwa 2010. Daga nan aka sake zabenta a dai wannan mukami daga watan Maris na 2010 har zuwa watan Maris na 2012 insha Allahu.