Cikakken Tarihin Yakubu Muhammad
Yakubu Muhammad na daya daga cikin shahararrun Jaruman Kamfanin shirya fina-finan Hausa dake Kano dakum Kamafanin Shirya fina-finan Turanci dake kudu.
Haka kuma Produsa ne kuma darekta a Kamfanin.
An haifi Yakubu Muhammad a ranar 25 ga watan Maris din shekarar alib 1973.
Shiga Masana’antar Fim
Ya shiga Kamfanin Finan-finan Hausa dake Kano a shekarar alib 1998, a mai rubuta fina-finai, sannan ya fara fitowa a Fim dinsa na farko mai suna Gabar Cikin Gida tare da babban abokinsa Sani Musa Danja a shekarar 2013.
Haka kuma nan ya shiga masana’antar Shirya Fina-finan Turanci dake Kudu a shekarar 2016, yayin daya fito a Fim dinsa na farko mai sun Son of Caliphate da kuma fim mai suna Shuga Naija tare da abokiyar aikinsa Rahama Sadau.
Wakokinsa
Yakubu Muhammad yayi wakoki sama da guda 1000 yayin da akayi amfanin da wakokin nasa a fina-finan Hausa sama da 100, sai kuma wasu da akayi amfani dasu a fina-finan turanci sama da guda 40.
Wasu Mukamai na Wasu Manyan Kamfononi Dayake Rike Dasu.
Jakada a Kamfanin Wayar Sadarwa na GLO,
Jakada a Kamfanin SDCs, sai kuma
Kamfanin Nescafe dake Najeriya.
Lambar Girma.
Yakubu Muhammad yasamu lambar yabo da yawa ciki harda labar girma daga City People Entertainment dakuma Nigerian Entertainment.
Dana Sanin shirin wani fim da ya fito.
A ranar 13 ga watan Satumbar shekarar 2020, ne dai yayi da nasanin fitawarsa a wani Fim din Kudanci mai suna Fatal Arrogance, wanda ya fito a mazaunin dan Shai’a.
Wanda hakan ya batawa masoyansa rai har ya janyo suka dinga zaginsa.