Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Hamisu Breaker

Hamisu Breaker Asalin sunan sa shine Hamisu Sa’id Yusuf amma mutane sun fi saninsa da (Hamisu Breaker) kuma sunan na Breaker ya samo asaline a lokacin da yana yin wani salon rawa da ake kira breaking tun a baya kafin asan shi a matsayin mawaki. Shahararren mawakin hausa ne musamman waƙoƙin soyayya wanda sunan sa ya hadu a Najeriya.

INDA AKA HAIFI HAMISU BREAKER.

An haifi Breaker a shekarar 1992 a Dorayi da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano Najeriya.

MATAKIN KARATU.

Ya halarci makarantar firamare da sakandare a Dorayi duk da har zuwa yau mawakin babu wani rahoto da yake nuni da ya cigaba da karatun jami’a.

LOKACIN DAYA FARA WAKA.

Breaker ya fara Waƙa ne tun lokacin yana makarantar sakandare kuma ya yi waƙoƙi da dama kafin ya fara fitar da album Kuma waƙar sa da ta yi tashe sama da ko wacce ita ce Jaruma musamman a cikin Hausawa. A wannan shekara ta 2020, Jaruma ita ce waƙar Hausa ta soyayya da aka fi kallo da sauraro domin saida takai wani mataki a YouTube da babu wata waƙar da ta taɓa kaiwa a ƙanƙanin lokaci a tarihin waƙoƙin hausa.

To wannan shene tarihin mawaki kuma jarumi a masana antar kannywood hamisu breaker kuci gaba da kasancewa da shafin mu mai albarka wato manuniya.com mungode da ziyarar ku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button