Biography / Tarihi
Cikakken Tarihin Feezy
Abdulhafiz Abdullahi (wanda aka fi sani da Feezy) Ya kasance mawaƙin Nijeriya. An haifeshi a garin Kaduna dake ƙasar Nijeriya a ranar 15 ga Satumba na shekarar 1997.
Sunansa:Abdulhafiz Abdullahi
Haihuwa15 ga Satumba, 1997
Jaha:Kaduna
Kasar asali Najeriya
Makaranta: Jami’ar Ahmadu Bello
Feezy Yayi makarantar firamare da sakandare a makarantar gwamnati na Kaduna Capital School dake Malali a Kaduna, yayi kuma karatunsa ta jami’a a bangaren ilimin kwamfuta a Jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zariya.
Feezy ya fara waƙoƙin gambarar Hausa ta zamani Hausa HipHop, da pop a cikin ƙungiyarsu ce ta Yaran North Side (YNS).
Wasu daga waƙoƙinsa sun hada da:
An Fara Physics: tare da Geeboy da Wiz mo),
Lies: tare da Sagy da Mr Kebzee
Spy
Raina Ni
Toyfriend
Lolo
Yo Baby