Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Daddy Hikima Abale

Daddy hikima (Adam Abdullahi Adam) wanda aka fi sani da Sanda ko abale shine babban jarumin Kannywood dake haskawa a yanzu a masana’antar fim.

Sanda ya fito a cikin jerin fina-finan Hausa sama da 20 a shekarar 2022, wanda hakan ya kara masa farin jini a arewacin Najeriya da wasu kasashen ketare.

Kaɗan Daga Cikin Tarihin Daddy Hikima Abale

Daddy hikima (Sanda) haifaffen (16 Maris, 1991) a jihar Kano ta Najeriya.

Ya samu satifiket din firamare da sakandire duk a Kano bayan ya shiga makarantar koyon aikin jinya da ungozoma.

Daddy hikima ya shiga harkar fina-finan Hausa a shekarar 2020 inda ya shahara bayan ya fito a wani fim mai suna ADUNIYA.

Aduniya shiri ne na Hausa wanda Tijjani asase wanda aka fi sani da KANABARO ya shirya kuma ya bada umarni a cikin fim din.

Shekarun Daddy Hikima Abale a Duniya

Tun daga 2022, daddy hikima yana da shekaru 31. An haife shi a ranar 16 ga Maris, 1991.

Abun da Daddy Hikima Abale ya mallaka a asusu

A cewar wasu majiyoyin yanar gizo, daddy hikima yana da kudin da ya kai naira miliyan uku.

Takaitaccen Bayani Game Da Daddy Hikima Abale

  • Full Name Adam Abdullahi adam
  • Other Name Sanda, Abale and Ojo
  • Date of birth 16th march, 1991
  • Age 31 years old
  • Place of birth Kano state
  • Nationality Nigerian
  • Tribe Hausa


Religion Islam

Language spoken Hausa and English
Movies Sanda, Aduniya, Haram, Asin DA asin, Uku sau uku, labarina, farin wata, Na ladidi, yan Zamani, makaryara and etc.
Net worth N3 million

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu