Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Ali Nuhu

Ali Nuhu An haife shi a ranar 15 ga watan Maris a shekarar 1974 a Jihar Borno. Ya kasance Shahararren jarumin fina-finai, kuma mai shiryawa tare da bayar da umarni na fina-finan Hausa wato Kannywood da Turanci a Najeriya wato Nollywood, Jarumin wanda ake ma lakani da Sarki musamman ma a masana’antar Kannywood.

Shahararre ne a cikin dukkan jarumai na fina-finai musamman na Hausa wato Kannywood, Sarki Ali Nuhu ya yi aure ne a ranar 28 ga watan disamban , shekarar 2003.

Farkon rayuwa

An haifi Ali Nuhu a Maiduguri, jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya. Mahaifinsa Nuhu Poloma daga Balanga gari Jihar Gombe da mahaifiyarsa, da Fatima Karderam Digema daga Bama gidan gwamnatin jihar Borno. Ya girma a Jos da Kano.

Ilimi

Ya yi karatu a Jami’ar Jos, Bayan karatun sakandare, ya sami digiri na farko a fannin ilimin fasaha daga Jami’ar Jos. Yayi bautar kasa a Ibadan da ke jihar Oyo. Daga baya ya halarci Jami’ar Kudancin Kalifoniya don yayi kwas a fagen shirya fina-finai da fasahar sinima.[4]

Sana’ar fim

Ali Nuhu ya fara fitowa a fim ne a shekarar ta 1999 mai suna “Abin sirri ne”. An fi saninsa da rawar da yake takawa a “Sangaya” wanda ya zama ɗayan finafinan Hausa da suka fi samun kuɗi a lokacin. Ali Nuhu ya fito a fina-finai da dama, wadanda suka hada da Azal.

Jarumin Maza, da Stinda a matsayin fitaccen Jarumi a wajen bayar da gudummawa a yayin bikin bayar da kyaututtuka na African Movie Academy a (2007). A shekarar ta 2019, Ali Nuhu ya yi bikin cikarsa shekaru 20 a masana’antar nishadantarwa. Ya fito a fina-finai kusan dari biyar (500).[5]

Mabiya

inda akayi ittifaki akan yana da mabiya a Twitter sama da 140,000 da kuma mabiya a Facebook sama da 1,200,000 da kuma wasu a shafin Instagram sama da 1,000,000.[6][7]

Fina Finai a Kannywood

(BT) na nufin Ba Tabbas, ma’ana babu tabbacin kwanan wata da shekarar da fim din ya fita. Yayin da akwai wasu kuma da ake da tabbacin kwanan watan fitar su.

  • Abaya BT Alhini BT
  • Abin Sirri Ne 1998 Ali BT
  • Alhini BT Alkebba BT
  • Ali BT
  • Alkebba BT
  • Ambato BT
  • Aska Tara BT
  • Zuwa Da Kai BT
  • Uwar Miji BT
  • ‘Ya ‘Ya Na BT
  • Ina Miji Na? BT
  • Gambiza BT
  • Namijin Duniya BT
  • Dama da Hauni BT
  • Ga Fili Ga Mai Doki BT
  • Masu Aji BT
  • Zo Mu Zauna BT
  • Mashi 2003
  • Gida da Waje BT
  • Yanayi BT
  • Farin Wata BT
  • Sakayya 1998
  • Harafin So BT
  • Zuciya Ko Ruhi BT
  • Sangaya 2000
  • JIGAL 2002
  • Bashin Gaba BT
  • Mai Gadon Zinare BT
  • Ragowar Yaki BT
  • Kishin Mata BT
  • Jurwaye BT
  • Fitilar Dare BT
  • Rana da Wata BT
  • Umarnin Uwa BT
  • Gadan Ga BT
  • Sabon Shafi BT
  • Hawan Girma BT
  • Khalid BT
  • Maraichi BT
  • Har Abada BT
  • Qiyasi BT
  • Shamsiyya BT
  • Tawakkali BT
  • Raliya BT
  • Maryam Diyana BT
  • Rawani BT
  • Ban Ga Masoyi Ba BT
  • Gidan Iko BT
  • Zamba BT
  • Kamilalla BT
  • Nazari BT
  • Garinmu da Zafi (Dawo-Dawo) BT
  • Bilal BT
  • Mujadala BT
  • Bahaushiya BT
  • Rariya 2017
  • Dangin Miji 2017
  • Ba Tabbas 2017
  • Mansoor 2017
  • Zuciya Da Hawaye 2017
  • Wacece Sarauniya? 2017
  • Jarumta 2016
  • Mu’amalat 2016
  • Dattijo 2016
  • Shinaz 2016
  • Igiyar Zato 2016
  • Halacci 2015
  • ‘Yar Tasha 2015
  • Wutar Gaba 2015
  • Bani Bake 2015
  • Gamu Nan Dai 2015
  • Uba da ‘Da 2015
  • Baya da Kura 2015
  • Ba’asi 2015
  • Sallamar So 2015
  • Kurman Allo 2015
  • Nasibi 2015
  • Hanyar Kano 2014
  • Sirrin Da Ke Raina 2014
  • Mai Dalilin Aure (Match Maker) 2014
  • Jinin Jiki Na 2014
  • Garbati 2014
  • ‘Ya daga Allah 2014
  • Idan Hakane 2014
  • Kanin Miji 2014
  • Mati da Lado 2014
  • Sai a Lahira 2014
  • Munafikin Mata 2014
  • Duniyar Nan 2014
  • So Aljannar Duniya 2014
  • Hujja 2014
  • Hakkin Miji 2014
  • Andamali 2013
  • Dakin Amarya 2013
  • Nadawo Gareki 2013
  • Wani Gari 2013
  • Da Kishiyar Gida 2013
  • Haske 2013
  • Lamiraj 2013
  • Jarumin Maza 2013
  • Fari Da Baki 2013
  • Zuri’a 2013
  • Mai Jego 2013
  • Mai Farin Jini 2013
  • Halisa 2013
  • Matar Jami’a 2013
  • Kudi A Duhu 2013
  • Madubin Dubawa 2012
  • Gani Gaka 2012
  • Wani Hanin 2012
  • Kudi A Duhu 2012
  • Son Zuciya 2012
  • Dan Marayan Zaki 2012
  • Kara da

Lamban girma

Ali Nuhu yana daga cikin jaruman fina-finan Hausa wadanda ke gaba-gaba wajen samun gagarumar nasarori a masana’antar ta Kannywood dama ta mutanen kudancin Najeriya wato Nollywood. Anan zamu kawo maku wasu daga cikin kyaututtukan da Ali Nuhu ya samu a harkar sa ta shirya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button