Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Aisha Najamu Izzar so

Aisha Najamu Izzar so ta kasance jarumar da tauraronta ke haskawa a masana’antar fina finan hausa wanda hakan yana da alaqa da shirinta na farko wanda ya shahara sosai musamman a Youtube wato shirin Izzar so wanda Lawal Ahmad da ali nuhu ke ciki kuma Nura Mustapha waye ya bada umarnin shirin.

Ita dai Aisha Najamu Izzar so an haifeta ne a garin jigawa 12 August, 1997 tayi karatun primary da sakandare a garin na kano kuma ta cigaba da karatu a jami’ar Maiduguri inda ta karanci Business Administration.

Allah ya taimaketa da samun nasara na harken tauraro tun a film dinta na farko wato izzarso duk da cewa ta fara futowa ne a wakoki kafin ta fara film, a cikin tattaunawa da tayi da BBC Hausa jarumar ta bayyana cewa izza da take nunawa a wannan shiri na izzarso ba halinta bane yanayi ne kawai na acting.

Duk da cewa wasu suna min kallon mace mai izza da girman kai a fili kamar yanda suke gani na ina taka rawa a film, alal hakika haka ba halina bane, na sami matsala wajen amincewar iyayena akan nuna musu muradina na fara film, da farko basu yarda ba amma daga bisani da suka fahimci shine mafi alheri a gareni.

Sai suka aminta da na fara harka Hausa film, Aisha Najamu Izzar So ta bayyane cewa ta taba aure kuma tanada yara, amma duk lokacin da Allah ya kawo mata wani mijin babu shakka zatayi aure kuma idan ta tuna cewa ta taba aure harda yara abin yana matukar faranta mata rai domin ko a yanzu tayi nasarar rayuwa domin ina kammala sakandare akayimin aure.

Jarumar ta izzar Aisha Najamu so ta cigaba da bayani inda ta bayyana kalubale da ta fahimta alokacinda ta wallafa wata waka domin nuna farin cikinta ga zagayowar ranar haihuwar sayyidina Ali, wanda hakan ya ja mata magana sosai har wasu suke jifanta da cewa ita yar shi’a ce wanda hakan bai mata dadi ba ko kadan.

kuma daga cikin abinda ke faranta mata rai shine inta tuna irin arziki da alheri da take samu yanzu ta dalilin film wanda take iya daukar nauyin kanta da na iyayenta, kanne harma da ‘yan uwa da abokan arziki, hakan yana faranta mata rai sosai kuma tana godema Allah da wannan baiwa da yayi mata.

a karshe tayi kira ga mata inda ta nuna cewa duk yanda mutum ya shigo film to ahaka abubuwa zasu rinka bayyana masa, domin ita tashigo da niyyar sana’a ne ba lalata ba kuma ta dauki film na hausa a matsayin sana’a don hakane yasa babu wani da ya taba zuwa mata da magana na iskanci ko lalata.

Jarumar ta izzar so Aisha Najamu ta rufe jawabinta da kin amsa tambayarda akayi mata na ko zata iya auren dan film din hausa? inda ta nemi da a bar maganar kawai.

kucigaba da kasancewa da shafin mu mai albarka mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button