Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Rantsar Da Tinubu – Sarkin Musulmi
Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Rantsar Da Tinubu – Sarkin Musulmi.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi wa gwamnatin da ke tafe addu’a don samun nasarar tafiyar da al’amuran kasar nan.
Sarkin Musulmin wanda ya bayyana haka yayin wani taron tattaunawa da sarakunan gargajiya da na addini a ranar Laraba a Abuja, ya ce kowa ya sani cewa sabuwar gwamnati za ta fara aiki a ranar 29 ga Mayu ko ana so ko ba a so.
Taron da Bankin Duniya ya shirya an tsara shi ne don samar da hanyar da za a bi domin bunkasa jari a kasar nan musamman ilimin yara mata.
Sarkin Musulmin wanda ya bukaci mahalarta taron da kada su yi watsi da shawarar kawo karshen auren ‘ya’ya da sauran abubuwan da ke kawo cikas ga ci gaban yaya mata.
Ya kara da cewa sarakunan gargajiya suna da muhimmiyar rawar takawa wajen ci gaban al’umma, a don haka ya tabbatar da cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen bayar da hadin kan da ya kamata don cimma burin da aka sanya gaba.
Jam’iyyar PDP ta dakatar da duk wasu daukar matakan ladabtar da ‘ya’yanta kan ayyukan da suka yi na kin jinin jam’iyyar a zaben daya gabata na 2023.
Daukar matakin jam’iyyar wani ci gaba ne a kokarin da shugabannin jam’iyyar na kasa ke yi na sanya da’a tare da samun cikakken sulhu a jam’iyyar.
Jam’iyyar tayi hakanne domin kafa wani kwamiti da zai duba duk wasu batutuwan da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka yi na rashin da’a da cin amanar jam’iyyar a zaben.
Jam’iyyar PDP ta dakatar da duk wasu daukar matakan ladabtar da ‘ya’yanta kan ayyukan da suka yi na kin jinin jam’iyyar a zaben 2023 da aka kammala.
Wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na kasa Debo Ologunagba ya fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa matakin na NWC wani ci gaba ne a kokarin da shugabannin jam’iyyar na kasa ke yi na sanya da’a tare da samun cikakken sulhu a jam’iyyar