Labarai

Ni momee gombe nakeso da aure ba rakiya musa ba dan haka tafita acikin rayuwata….

Ni momee gombe nakeso da aure ba rakiya musa ba dan haka tafita acikin rayuwata….

Yan Uwana Mata barkan mu da sake saduwa daku a cikin wannan fili namu mai matukar farin jini, wato Sirrin Gyaran jiki… Kamar yadda kuka sani shi wannan shiri a na yin shi ne don matan aure zalla domin basu shawarwari ta kowane bangare na rayuwarsu ta yadda za su samu su gyara zaman takewarsu da mazajen da mu’amalar su ta bangaren girki, tsafta, gyaran gida da gyaran jiki.

Irin abubuwan daya kama mu mata mu dinga ci domin karin ni’imar mu da gamsuwar mazajen mu, da ma duk wani abu daya shafi rayuwar ya mace. Da fatan za ku dinga bibiyata a cikin wannan shiri.gurin da nayi kuskure sai nace Ina neman afuwar ubangiji da afuwar ku domin ajidan ci irin na dan Adamtaka, gurin kuma da nayi dai dai Sai nace Allah ya hada mu a ladan baki daya.

Da farko Lallai ya kamata ku gane cewa infection yanada wuyan magani domin maganine da se andauki lokaci anayi kamin ya warke gaba daya,inda sansamune ku dauki lokaci kaman wata 6 ajere koma fiye shine zakiga kin maganceshi gabadaya amma in zaki fara ki bari to lallai zaki dade kina magani baki maganceshi gabadayaba. kuma lallai wacce take da miji sai sunyi magani su biyu amma intasah magani ita kadai kamar tayi a bandane don suna kara saduwa da mijin ata kara.

A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya. Yana maganin budewa da kaikayi.

A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa, mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Ya na fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari.

A samu Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button