Labarai

Mene Ne Hukuncin Wanda Ya Yi Buda-Baki Da Jima’i?

Amsawar Dakta Jamil Zarewa, Jami’ar ABU

Assalamu alaikum. Malam barka da warhaka, da fatan kana nan lafia. Malam mene ne hukuncin wanda ya yi azumi amma bai yi buda-baki ba, ma’ana bai sha ruwa bayan ladan ya kira sallah ba, sai kawai ya yi jima’i da matarsa, ma’ana maimakon ya ci wani abu ko ya sha, sai ya fara da yin jima’a, shin yaya azuminsa?

Wa alaikum assalam, Azuminsa ya yi daidai, mutukar ya sadu da ita ne bayan rana ta fadi. Annabi s.a.w ya yi umarni a yi buda baki da dabino ga wanda ya samu dama, in ba hali kuma a yi da ruwa kamar yadda ya tabbata a Hadisai.

Abin da ya gabata yana nuna cewa: Yin buda-baki da dabino ko ruwa shi ne sunna, saidai wanda ya fara da jima’i azuminsa ya inganta, tun da Allah ya halatta masa jima’i a daidai wannan lokacin kamar yadda aya ta: 187 a suratul Bakara ta nuna hakan.

Allah ne mafi sani.

Mace Za Ta Iya Yin I’itikafi?

Assalamu Alaikum, malam menene hukuncin ittikafin mata a musulunchi?

Wa alaikum asssalam, ya halatta mace ta yi i’itikafi, saboda matayan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun yi i’itikafi kamar yadda ya zo a sahihil Bukhari. Yana daga cikin ka’idoji a usulul fikhi duk hukuncin da ya zo a sharia yana hade mata da maza, sai idan an samu dalilin da ya kebance maza kawai. I’itikafi ibada ce tabbatacciya a musulunci wacce Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aikata ta saboda neman kusanci da Allah a watan Ramdhana, babu bambanci tsakanin mace da namiji wajan koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a wannan ibadar, saidai kar matar aure ta fita sai ta nemi iznin mijinta.

Allah ne mafi sani.

Mace Za Ta Iya Tafsiri Da Lasifika?

Mutane da yawa sun tambaye ni game da hukuncin tara mata a masallaci, mace ta yi musu TAFSIRI da lasifika, shin ya halatta?

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : “Duk lokacin da mutane suka hadu a Dakin Allah suna kokarin fahimtar littafin Allah, natsuwa za ta sauka gare su, kuma Mala’iku za su kewayesu, sannan Allah zai ambace su a wajan wadanda suke tare da shi”. Muslim hadisi Mai lamba (7030).

Hadisin da ya gabata Yana nuna halaccin mace ta karantar da Alku’rani a masallaci saboda hadisin bai bambance tsakanin namiji da mace ba.

Sai dai idan mun bi mazhabar malaman da suka inganta hadisin Amru Dan Hazm akwai turnuku wajan mace ta yi Tafsiri a watan Azumi, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: “Kar wanda ya taba Kur’ani sai mai Tsarki” domin babu yadda za a yi mace lafiyayyiya mai matsakaitan shekaru, ta kammala Ramadhana uku ba ta yi AL’ADA ba.

Malaman Malikiyya suna fifita mace ta yi karatun Sallah a asirce har a sallolin da ake bayyanawa, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umarci mata da yin tafi idan liman ya yi rafkannuwa, idan suna tare da maza don kar a ji muryarsu, kamar yadda Bukhari ya rawaito, wannan sai ya nuna ba a son mace ta daga muryarta, to ina kuma ga Lasifikar da za ta isar da sakon ga maza, ga kuma ‘yan social media a gefe wadanda za su yada hotunanta da muryarta a duniya?

Duk da cewa wasu daga cikin mata magabata suna koyar da maza da mata, sai dai ba a bainar jama’a suke yi ba cikin daga murya, wannan ya sa yin kiyasi a kan aikinsu ba zai tafi ba, saboda sababi da illar sun yi hannun riga.

Ayoyi da hadisai da yawa sun nuna halaccin yin wa’azi ga mace, sai dai akwai bambanci tsakanin wa’azi da kuma tafsirin Kur’ani, saboda tafsirin Kur’ani yana wajabta taba shi yayin nazari da kuma karantarwa, hakan kuma haramun ne ga Mai haila bisa hadisin Amru dan Hazm da ya gabata.

Yana da kyau mata da maza masu yin Tafsiri su yi taka-tsantsan wajan fassara zancen Allah saboda darajar littafin da kuma girman danganta wa Allah abin da mutum ba shi da tabbas.

Ban da tafsirin Alkur’ani akwai hanyoyi da yawa na samun Lada a Ramadhana.

Source: kannywoodstyle.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button