Shin Dagaske Kuros Ne A Jikin Rigar Minister Isah Ali Pantami?
Shin Dagaske Kuros Ne A Jikin Rigar Minister Isah Ali Pantami?
Wani shafi sada zumunta na facebook mai suna Taƙiyya izala ya wallafa hoton ministan harkokin sadarwa a Najeriya kuma shahararren malamin addinin Islama Dr Isa Ali Fantami.
Inda ya yi zargin cewa wai malamin ya sanya wata kwalliya a rigar jikinsa mai ɗauke da alamun Cross.
Sai dai idan mai karatu ya lura da kyau zai ga ba Cross neba Biro ne malamin ya soka a aljihunsa sai kuma kwalliyar aljihu ta gitta shi yasa ya nuna kamar Cross.
Amfanin Agwalima Ajikin Dan Adam
Akwai wasu tarin yayan itatuwa da ke da tarin alfanu sannan kuma basu da wata illa ga jikin dan Adam.
Sai dai mutane da dama basu san da haka ba hakan ne yasa muka lalubo maku wasu daga cikin amfanin agwaluma.
Wani sabon binciken kimiyya ya nuna cewa za a iya amfani da ganyayyaki da itacen Agwaluma wajen magance wasu cututtuka a jikin dan adam.
NCIKEN DA KIMIYYA SUKAYI AKAN AMFANIN
Binciken da Masana kimiyya sukayi akan Amfanin da Agwaluma keyi ga jikin Dan Adam.
Tabbass lafiya ita ce uwarjiki kuma kowa ya kwana lafiya shine ya so hakan.
Akwai wasu tarin yayan itatuwa da ke da tarin alfanu sannan kuma basu da wata illa ga jikin dan Adam.
Sai dai mutane da dama basu san da haka ba hakan ne yasa muka lalubo maku wasu daga cikin amfanin agwaluma.
Wani sabon binciken kimiyya ya nuna cewa za a iya amfani da ganyayyaki da itacen Agwaluma wajen magance wasu cututtuka a jikin dan adam.
1. Agwaluma na maganin zazzabin Malaria mai naci ko wanda bai jin magani.
Binciken wanda aka wallafa a kundin BMC Complementary and Alternative Medicine ya bayyana cewa wannan magani ka iya zama sabuwar karbabbiyar hanyar magance zazzabin duba da rashin nasarar da ake samu da sauran nau’ikan magunguna.
2. Agwaluma dai na dauke da sinadarin Vitamin C, wanda ke da matukar amfani a jikin dan adam.
3. Agwaluma na da matukar amfani ga mai dauke da juna biyu. Shan agwaluma na tsayar da amai da jiri wanda juna biyu ke haifarwa.
4. Sannan idan mutum baya so yayi kiba daya wuce misali sannan yana bukatar sinadarin gyaran idanu da zuciya toh agwaluma na taimakawa sosai wajen cimma hakan.
5. Yana kuma taimakawa wajen samun bacci cikin kwanciyar hankali. Sannan kuma yana rage ciwon gabbobin jiki.