Siyasa

Atiku ya lashe Tinubu, Peter Obi a Bauchi da kuri’u 109,913

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress, da kuri’u 109,913 a jihar Bauchi.


Manuniya ta ruwaito da yammacin ranar Litinin ne jami’in tattara sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Farfesa Abdulkarim Mohammed mataimakin shugaban jami’ar tarayya dake Dutse a jihar Jigawa ya sanar da sakamakon zaben.

Abdulkarim ya bayyana sakamakon zaben ne a dakin taro na Farfesa Mahmood Yakubu da ke hedikwatar hukumar zabe mai zaman kanta da ke Bauchi, cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa a jihar.

Da yake bayar da takaitaccen sakamakon zaben, jami’in tattara sakamakon zaben ya ce Atiku ya samu kuri’u 426,607 yayin da Tinubu, ya samu kuri’u 316,694.

Da yake bayar da takaitaccen sakamakon zaben, jami’in tattara sakamakon zaben ya ce Atiku ya samu kuri’u 426,607 yayin da Tinubu, ya samu kuri’u 316,694.

A cewar Abdulkarim dan takarar jam’iyyar

New Nigerian Peoples Party (NNPP), Rabiu Kwankwaso ya samu kuri’u 72,103 yayin da Peter Obi na jam’iyyar Labour ya samu kuri’u 27,373.

Mohammed ya ce wadanda suka yi rajista a jihar sun hada da: 2,749,268 yayin da wadanda aka amince da zaben su ne: 899,769.

Kuri’un da aka kada a cewarsa sun kai 853,516, kuri’u 29,030 da aka ki amincewa da su, kuma jimillar kuri’u 882,546.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button