Labarai
Saura Kwana 10 Zaɓe: Bamu da tsabar kudin da za mu gudanar da aikin zaɓe – INEC
INEC ta ce har yanzu babu kudi a kasa na gudanar da zaben Nijeriya
Hukumar zaben Nijeriya INEC, ta ce har ya zuwa yanzu babu kudi q kasa wanda za ta gudanar da babban zaben da ke tafe kamar yadda majiyar DCL Hausa ta jaridar Daily trust ta ruwaito.
Hukumar ta bayyana hakan ana sauran kwanakin 10 a gudanar da zaben shugaban kasa da na yan majalissu a tarayyar ta Nijeriya.
‘Yan Nijeriya dai na fama da karancin takardun kuɗi na N200 N500 da kuma N1000 tun bayan sauya fasalin takardun kuɗi da babban bankin kasar ya yi.