Ganduje Zai Soke Lasisin Bankuna Da Wuraren Sana’oin Da Basu Karbar Tsoffin Kudi A Jihar Kano
Ganduje Zai Soke Lasisin Bankuna Da Wuraren Sana’oin Da Basu Karbar Tsoffin Kudi A Jihar Kano.
Gwamnatin jihar Kano ta yi gargadin cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen soke lasisin gudanar da harkokin kasuwanci na manyan ‘yan kasuwa ko kuma daukar mataki kan duk wanda ya ki karbar tsohuwar takardar Naira a matsayin wajen ciniki daga al-ummar jihar.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya yi wannan gargadin a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Malam Muhammad Garba ya fitar, yace har yanzu kudaden na naira na nan a matsayin halastattu.
Yace kotun koli ta jaddada hukumcin wucin gadi da ta yi kan batun tsofaffin takardun kudin Naira da za a ci gaba da amfani da su tare da sabbi har sai an kammala bin matakai sa suka kamata.
Gwamnan ya yi nuni da cewa gwamnati ta lura da yadda wasu ‘yan kasuwa kamar manyan kantuna da bankuna da gidajen cin abinci da otal-otal da ‘yan kasuwa a kasuwanni da gidajen mai da tashoshi mota, da dai sauransu ke kin karbar tsohon kudi a hada-hadar kasuwanci.
Ganduje ya kara da cewa rashin amincewa da wasu ke yi da tsaffin kudin na kara dagula al’amura.
Gwamnan ya gwamnatin jihar Kano ba za ta nade hannunta ba, ta bar wasu masu son zuciya suna jefa mutane cikin wahala, yana mai yi kira ga al’umma da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu na halal tare da kai rahoton duk wanda ya ki karbar tsohuwar takardar Naira.